Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya shugabanci zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis.
Wannan dai shi ne karo na farko da ya jagoranci zaman majalisar tun bayan buɗe ta ranar 13 ga Yunin 2023.
Sanata Barau ya shugabanci zaman majalisar ne kasancewar shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio bai samu halartar zauren ba.
Sanata Akpabio ya zama sabon shugaban Majalisar Dattawa
Barau Jibrin ya tsaya takarar shugabancin Majalisar Dattawa
Mataimakin shugaban ya shiga zauren tare da rakiyar ragowar jagogori inda aka fara zaman da misalin ƙarfe 11:00am.
Ya na zama kan kujerar shugabancin Majalisar kuma sai takwarorinsa sanatoci suka ɓarke da sowa da tafi.
Wakilinmu ya rawaito cewa Sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa ya jagoranci zaman majalisar cikin nutsuwa da walwala.