✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sana’ar yankan taya ta yi min komai a rayuwa’

Alhassan Ahmed, magidanci ne mai shekara 55 wanda ya share sama da shekara 30 yana sana’ar yankan taya wadda ya ce a cikinta ya taso…

Alhassan Ahmed, magidanci ne mai shekara 55 wanda ya share sama da shekara 30 yana sana’ar yankan taya wadda ya ce a cikinta ya taso domin mahaifinsa ma sana’arsa ke nan. Kuma ya ce, sana’ar ta yi masa komai a rayuwa, kamar yada ya shaida wa Aminiya:

 

Aminiya: Yaushe ka fara sana’ar yankan taya?

Alhassan Ahmed: Wannan sana’a a cikinta na taso sama da shekara 30.

Aminiya: Sana’ar tana bukatar jari ne kafin a fara ta, idan tana bukata da nawa ka fara?

Alhassan Ahmed: Eh, tana bukatar jari ko da ba yawa, ni da Naira dubu 500 na fara, kuma ta habaka.

Aminiya: Wane irin rufin asiri ka samu a sana’ar?

Na samu rufin asiri sosai a sana’ar nan don da ita na sayi shago na yi aure na mallaki abubuwan rayuwa daban-daban.

Aminiya: Yara nawa ka koya wa sana’ar?

Alhassan Ahmed: Akalla yara biyar na ware su ma yanzu haka sun zama wadansu, suna cin gashin kansu da sana’ar ta yi musu rana.

Aminiya: Bayan ka ware yara biyar yanzu yara nawa suke cin abinci a karkashinka?

Alhassan Ahmed: Yara uku nake da su yanzu kuma dukkansu ’ya’yana ne.

Aminiya: Tunda sana’ar ta  yi maka  rana wane kira kake da shi ga matasa?

Alhassan Ahmed: Kirana ga matasa shi ne ko da suna karatu su nemi sana’a domin gwamnati ba za ta iya bai wa kowa aiki ba kuma sana’a ita za ta ba ka dama ta dogaro da kanka.

Aminiya: Wadanne abubuwa kuke yi da tayar?

Alhassan Ahmed: Muna yin takalman taya da damfa roba da ake sa wa a A-kori-kura da yake taimaka mata wajen daukar kaya mai nauyi da nauyin robobi da yawa.

Aminiya: Ka taba neman tallafin gwamnati don bunkasa sana’ar?

Alhassan Ahmed: Ban taba ba amma idan na samu ina so domin idan aka taimaka min sana’ar za ta bunkasa fiye da yadda take a yanzu.

Aminiya: Wane irin tayu kuke amfani da su?

Alhassan Ahmed: Manyan tayu na katafila da tirela har da na kananan mota amma Dunlop mai zare ba mai waya ba.

Aminiya: A karshe mece ce fatarka kan sana’ar?

Fatata ita ce kamar yadda sana’ar ta yi min rana nake dogaro da kaina, in da gwamnati za ta taimaka da ci gaban zai wuce haka kuma za a samu raguwar zaman banza a tsakanin matasa domin za mu ci gaba da koya musu sana’ar.