Ana iya cewa maganar da ake fada cewa sana’a sa’a ta yi daiai da kwatancen Murtala Rabiu, wani dan kasuwa da a iya cewa ya shiga sana’ar tuwon madara da kafar dama.
Da Naira 1,500 Murtala da ke zaune a garin Kaduna ya fara sana’ar tuwon madara, har ta kai ga yanzu yana juya miliyoyin Naira.
Shekara uku da suka wuce ne Murtala ya yi tunanin fara sana’ar tuwon madara wanda a wasu wuraren ake kira alawar madara, daya daga cikin kayan tande-tande a Arewacin Najeriya.
Ya ce bayan da ya da ya gabatar wa matarsa muradinsa, sai ta yarda za ta rika yin tuwon madarar, su rika kaiwa wurin kananan ‘yan tireda.
- ‘Buhari ya soke karin farashi ko ya ga bacin rai’
- Na rungumi kaddarar rasa auren diyar Buhari —Matashi
Ya yi tunanin yin hakan ne bayan ya lura akwai karancin tuwon madara a unguwar da yake; saboda haka shi da matar tasa suka fara yin tuwon madarar na leda wanda suka sa wa suna ‘Aunty Binta Milk’.
“Da na yi wa matata magana game da yin tuwon madara ta yarda sai na hada ta da masu shaguna”, inji shi.
Yadda sana’ar ta bunkasa
Ya ce sun fara sana’ar ne da jarin N1,500, a hankali abun ya bunkasa kuma yadda masu shaguna ke bukatarsa ta yi ta karuwa.
“Babbar ribar da muka samu da wata Sallah ce, sai muka yi tunanin amfani da ribar mu sayi buhun madara, to da ribar da muka samu ne muka fara yin tuwon madarar da yawa.
“Da sallar, matata ta yadda a yi na buhun madara buhu. Saboda haka sai muka sai muka nemo wasu mutum biyu su zo su taya ta kuma suka yarda.
“Ita tana hadawa su kuma suna yayyankawa kuma cikin ikon Allah aka sayar da shi gaba daya.
“Daga lokacin, sai muka fara sawa a mazubi leda mai kyau”, kamar yadda ya ce.
Ya ce maimakon yadda a baya suke sa wa a farar leda, sai suka koma amfani da leda ta musamman dauke da sunan tuwon madarar da sauran bayanai yadda ake wa kayan kamfani na cikin mazubin leda.
“Daga nan sai muka fara amfani da inji, muka sayi injin nika da na kwabi da na like leda domin aikin ya yi sauri.
“Sai ya zama muna iya yin buhu hudu a rana muna samun ribar N5,000 zuwa N10,000 a kowane buhu”.
A wannan mataki har sun fara kai tuwon madarar manyan shaguna a fadin Kaduna a jihohi masu makwabtaka na Katsina da Zamfara.
– Sirrin nasarar da aka samu –
Da aka tambayi Rabiu game da sirrin wannan gagarumar nasara, sai ya kada baki ya ce: “ciniki rabo ne, amma kyakkyawan shiri da kayata kaya da tallatawa da kuma ingancin kaya na da muhimmanci.
“Ni dai na dage ne a kan tabbatar da ingancin kayana”, inji shi.
Ya kara da cewa kyan mazubi shi ma sirri ne a kasauwanci, saboda haka ya shawarci masa sana’o’i da da ba wa ingancin kayansu muhimmanci.
Sai dai ya ce yanzu cinikinsu ya ragu sakamakon tasirin COVID-19.
Ya danganta raguwar cinikin da dokar kulle da gwamantoci suka sanya domin dakile yaduwar kwayar cutar.