✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar Sankira ta samu tagomashi a zamanance – Kabir Bahaushe

Wane ne Kabir Bahaushe? Sunana Comrade Kabir Sa’idu Bahaushe dandagoro, karamar Hukumar batagarawa a Jihar Katsina, Najeriya. An haife ni a garin dandagoro a ranar…

Wane ne Kabir Bahaushe?

Sunana Comrade Kabir Sa’idu Bahaushe dandagoro, karamar Hukumar batagarawa a Jihar Katsina, Najeriya. An haife ni a garin dandagoro a ranar 18 ga Janairun 1991.

Na yi dalibta a Makarantar Allon Marigayi Malam Shafi’i a garin dandagoro da kuma Madarisatul Ulumil kur’an dandagoro da kuma Tartilil kur’an da ke a Kofar kaura Katsina da kuma karatu a hannun Malam Usman dandagoro da wasu malaman daban.

Na yi karatun firamare a dandagoro Model Primary School daga 1997 zuwa 2002, daga nan na wuce zuwa makarantar sakandare ta Gobernment Rural Boarding Secondary School batagarawa, wacce ta koma Gobernment Science Secondary School yanzu, inda na kammala a 2008.

Na samu damar kammala karatun Digiri a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa da ke a Katsina a shekarar 2016, inda na karanci Ilimin Darussan Koyarwa da kuma Hausa (Education Hausa).

Na yi aiki da Mujallar Al-Irshad a shekarar 2012, ina kuma yin rubutu da aika rahoto a Mujallar Muryar Arewa da kuma yin rubutu a Jaridar Leadership Hausa kamar kuma yadda yanzu haka nake gabatar da shirye-shirye sama da iri bakwai a gidan Rediyon bision Fm 92.1 Katsina. Ana yin hira da ni a kafofin watsa labarai da dama, ina kuma rubuta ra’ayoyina kan lamurran yau da kullum a jaridu da mujallun Hausa. Ina kuma yin sana’ar MC watau Sankiran Zamani, ina gabatar da tarurrukan kungiyoyi da na kara wa juna sani ko tunawa da wani ko na karramawa da biki da suna da murnar zagayowar ranar haihuwa da dai sauransu da dama.

Ka kasance marubuci/Fim/Sankira. Yaushe ka fara wadannan harkoki kuma me ya ja ra’ayinka gare su?

To, rubutu na ji kawai ina sha’awarsa sai na fara rubuta takardun nasiha da jan hankali, ina rarrabawa a masallatai da Islamiyoyi, sai kuma ta dalilin sana’ar sayar da jarida da na yi a wajen Malam Rabi’u a Sabon Layi Katsina. Saboda ina yawan karantawa da kuma lura da salon su marubutan jarida da litattafai. Daga nan ne na samu aiki da Mujallar Al-Irshaad, har na zo Mujallar Muryar Arewa a 2012, na rika rubutu kan soyayya a shafina na ‘Taskar So.’ Daga baya na zama wakilinsu. Ina cikin jami’a kuma na gabatar da takarda a 2013 mai taken ‘Tarbabarewar Al’adun Hausawa Yau A Harkar Soyayya’ a taron kara wa juna sani na kasa da kasa, abin da babu dalibin da ya tabb yi, domin malamai ne kawai ke yi. Na ce zan iya, aka ba ni dama kuma na rubuta na gabatar.

Harkar fim kuma ina sha’awarta ne, sai dai na fi son zama mai daukar nauyi da shiryawa. Na taba fitowa a fim din daurin Zato, inda na yi addu’a ta musamman a shekarar 2015. Sai dai yanzu ina shirya wasanni ne a Jihar Katsina da manyan jaruman fina-finan Hausa a karkashin kamfanina na Kakaki Mobies, wanda wani reshe ne na Kakaki Unikue Awards Limited; inda nan gaba zuwa badi, idan Allah Ya yarda za mu rika yin manyan fina-finai. Kuma ina yin sharhi kan masana’antar a kafafen watsa labarai.

Batun MC (Sankiran Zamani) kuwa, na fara shi ne tun a 2014 , inda ina jami’a aka ba ni dama na rika gabatar da tarurruka saboda ba kowa ke iyawa ba (wasu da yawa na jin tsoron magana a gaban jama’a masu yawa). Da farko wani ne kawai ya kasa, aka ce na karba kuma na ci gaba lafiya lau. Sai ta kai ga har aka rika gayyatata a waje ina yi ina samun abin rufin asiri.To tun da ana samun kudi sai sha’awar son yin sana’ar ya kama ni, daga nan zuwa yanzu abin ya yi ta karbuwa. Wurare da dama ana gayyatata da kuma manyan tarurruka wanda ban taba tunanin ma za a iya gayyatata su ba gaskiya ko a mafarki.

Sana’ar Sankira a zamanance (MC) bakuwa ce a kasar Hausa. Shin yaya take kuma wadanne kalubale kake fuskanta wajen tafiyar da ita?

Eh, gaskiya ne. Yadda take, MC na nufin Master Of Ceremony watau Mai Tafiyar da Taro baki daya. Kuma shi MC shi ne ke yin magana a kan komai da duk abin da za a yi a cikin taro. Yana sanya mutane su yi shiru ya kuma dauke masu hankali da maganganun hikima ko na ban dariya da kuma ilimantarwa da fadakarwa kan taron da ake gudanarwa ko na mene ne don ya yi armashi. Yana yin karin haske ko takaitawa ko fassara maganganun da masu jawabi suka yi bayan ya gabatar da su ya bayyana ko su wane ne. Shi ne kuma ke ba da lokacin yin komai a taro, na cin abinci ko na tsawon magana da shakatawa. Sannan uwa-uba, ko ba abin da za a yi a lokacin ko an samu jinkiri yana da damar rike taron da baiwar da yake da ita.

kalubale ga duk mai yin sana’ar shi ne, ba kowa ya iya fahimtar kima da darajarta ba saboda wasu sai su dauka kamar mutum maroki ne, ko kuma ai tun da cikin iyalanmu ko ofis dinmu ko makarantarmu da sauransu akwai wanda yake iya Magana, ba dole ne sai mun dauko wani mun biya shi ba ya yi mana sankira. Kai wasu ma ba su san wane ne MC ba kamar yadda kai ma a tambayarka ka ce sana’a ce bakuwa. Haka wani kawai sai ya kira ka ana gobe za a yi taro ko biki, ya ce ka zo ka yi masa, ko kuma kawai mutum ya yanke maka farashi da kansa na aikinka. Ko kana cikin magana wani na cikin hidimar ya nemi ya amshi lasifika ya ba da wata sanarwa ko wani sako, ko kuma irin yadda masu taro ba su ba da komai a rubuce kafin ranar, sai dai a baki ko kuma kowa ya zo ya zagaye ka yana cewa ce a yi kaza ko a sa mana waka kaza, da kuma irin Dj (masu saka kida da ba ta sauti da kayansu) da mawaka da ’yan rawa da makada za su ga kamar ka hana su dama alhali ba a tsara da su ba. Ko kuma masu taro su gayyato mutane da yawa.

Ko littafi nawa ka rubuta, fim nawa ka fito ciki, ko akwai wanda ya shiga kasuwa cikinsu?

Na fi yawaita rubutu a jaridu gaskiya da kafafen sadarwar zamani (Social Media) amma akwai littattafai guda hudu da na fara rubutawa kuma zan sake su cikin shekara daya da rabi ko biyu idan Allah Ya yarda, daya bayan daya. Don haka babu wanda na saki ballantana ya shiga kasuwa, sai dai an buga a jaridu da dama da lissafa su zai yi wuyar gaske.

Fim daya na fito a ciki na daurin Zato, duk da ina zuwa lokeshin da dama a nemi na shiga na ki yarda, ko kuma zan yi amma wani abu ya ratsa na fasa ko ban je ba saboda yawan hidimomin da nake cikinsu. Nan gaba idan dama ta samu akwai yiwuwar na yi, musamman ma zan fito ne a matsayin MC, tun da nan na fi wayau.

A matsayinka na matashi, me za ka ce wa matasa dangane da sana’arka ta Sankiran Zamani (MC)?

To, gaskiya sana’ar MC sana’a ce mai cikakkiyar dama da sa’a, mai jawo daukaka matuka. Ban mantawa ina jami’a muna cikin yin jarabawa kuma ba ni da ko sisi kawai aka kira ni MC, aka biya ni kudade da yawa da suka ishe ni har na gama jarabawar cikin walwala da jin dadi, lokacin ma ba wanda ya san ina yi. Sana’a ce da ta sanya ni haduwa da shahararrun mutane da manyan mutane da jami’an tsaro da ’yan siyasa da mawaka da ’yan fim da sauransu.

Idan ina tafiya ko na je wani waje, inda ba na tunanin an san ni, kawai sai in ji an ce MC, bayan kudade da ba za ka iya kayyade su da ake ta samu.

Ke nan matashi zai iya dogaro da kansa da ita, kuma gaskiya yawanci baiwa ce. Ko da mutum ya koya idan ba shi da kazar-kazar da sarrafa harshe ba zai yi tasirin da zai ratsa zukatan mutane ba su rika gayyatarsa sauran abubuwansu.

Ni yanzu alhamdu lillahi, ina da wadanda ke koyo a wajena da kuma masu yi mini hidima, tun da ina da manaja da ake neman aiki da ni ta hannunsa kuma shi ke fada mani tarurrukan gaba, da mai rike mani jikka da wayoyina da rarraba katin adireshina da wasu kuma MC din, wadanda bukukuwa suka mani yawa nake tura su, su ma su yi.

Mene ne burinka a rayuwa dangane da wannan sana’a taka?

Burina Jama’a su fahimci tare da gane muhimmancin da muke da shi a yayin kowane taro, har sai sun rika gayyatar wanda ya iya ba kowa ba. Don da haka ne sana’ar za ta ci gaba da kuma kara daraja da tagomashi da kanshin dan goma. Sannan ina da burin in kirkiri wata kungiya ta masu yin harkar don kara wa juna sani, don wasu ba su iya komai ba kuma ba su neman sani ko koyo, haka nan kawai suke rike kuttun magana.

Domin ni ina karuwa da wasu masu yi idan suna yi, kamar MC Big Boy na Kaduna da Abbas Sadik da wasunsu kuma ina yin karance-karancen harkar a yanar Gizo don karin ilimi.

Wane kira gare ka ga abokan sana’a da jama’a da kuma gwamnati?

Kirana ga abokan sana’ata shi ne, a rika neman ilimin harkar nan, a kauce wa duk wani abu da zai zubar da mutunci kamar rokon kudin fansar ango da amarya ko wani. Ka yi duk cajin kudin da za ka yi a lokacin da aka gayyace ka ba bayan ka zo taro ba. Kuma a rika yawaita dinka suturu da kuma fahimtar kowane taro da yadda ake gabatar da shi da kuma irin shigar da ake yi tare da mutunta lokaci. Sannan a cire hassada da bakin ciki, a kuma san me za a rika fada. Don na san wani MC ana cikin taro ya yi wata maganar da ta sa kowa ya watse, wanda ba haka aka so ba.

Jama’a kuma a rika biki da kowane irin taro da mu, in dai ba na mutuwa ba ne ba. A rika nemanmu da wuri ba sai wuri ya kure ba, a kuma biya a mutunce tun kafin a yi, a rika ba mu tsare-tsaren taro da wuri. A kuma rika bari mai aiki ya yi aikinsa ban da takura ko zakalkalewa, tunda aka biya mutum ya yi to sai a mutunta wannan kimar da yake da ita.

Kodayake mu sana’armu babu ruwanta da jari sai sutura kawai da samun horo, tunda magana ce jarinmu. Muna bukatar gwamnati da ta yi kokarin daukar nauyin shirya tarurrukan kara wa juna sani, kuma a rika gayyatar masu kwarewa ba dole sai ma’aikatan gwamnati ba a tarurrukan gwamnati kamar yadda aka saba.