✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar kitso ta kare min mutuncina – Maimuna Abubakar

A kasar Hausa kitso ya zama sana’a ga wadansu mata da ke yi wa sauran ’yan uwansu mata a duk lokacin da bukatar haka ta…

A kasar Hausa kitso ya zama sana’a ga wadansu mata da ke yi wa sauran ’yan uwansu mata a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Mai wannan sana’ar ita ake kira mai kitso. Aminiya  ta tattaunawa da wata mai sana’ar kitso kwararriya da ke zaune a Unguwar Gawon Dannunu, a Tudun Wadan Sakkwato mai suna Maimuna Abubakar, inda ta bayyana yadda sana’ar take:

Yaya kitso yake a kasar Hausa?

Akwai nau’o’in kitso da dama da muka samu kakanninmu na yi duk da cewa a da ba wasu nau’o’in kitso suke da su masu yawa ba. Kawai mace ta yi kitso, amma daga baya an samu wasu nau’o’in kitso kamar Zanen Yawo, Kwandon Kifi, Tukkuwa, Shaku,  Tsiro Shida da Mai Ayaba. Daga baya kuma an samu karin wasu da suka hada da  Kabarin Murtala, Gadar Jebba  da Juyin Mulki.

Cudanyarmu da wasu al’ummomi da kabilu a wannan zamani ya sa wasu nau’o’in kitso sun shigo kasar Hausa da suka hada da Ibira Style (Salon Ibira) da Ghana Weabing, da Two Babies da Kiss Me, da Police Cap da sauransu.

Kitso zai zama ko dai kitse ko weabing ya danganta daga wurin daukar, wato yadda za a saka kitson ko dai ya zama gaba-gaba ko a fara shi daga baya.

 

Wadanne abubuwa ake bukata  domin yin kitso?

A kowane lokaci dole ne ya kasance akwai tsinke (ko kibiya), wanda yake kamar matsayin aska ga wanzami, ba yadda za a yi kitso ba tare da tsinke ba, dole kuma ya zama mai tsini sosai, ban da marikinsa, kuma yakan bambanta  daga wannan zuwa wancan. Sai kuma mashacin kai ko matsefi, wadannan su ne manya. Sai kuma man shafi, can da kakanninmu suna amfani da man kade ko man shanu, wanda ’yan matan yanzu ke ganin suna sa wari a kai, sai dai yanzu da aka fara inganta man kade domin ya yi daidai da zamani wato man shea butter.

A yanzu akwai nau’o’in man kitso ba su kirguwa, ya danganta daga abin da mace take so, akwai na gyaran gashi da tsawon gashi da masu maganin amosanin ka da na laushin gashi. Wadannan nau’o’in man kitson sun hada da Kuza, coconut oil, pick oil, shea butter (man kade) formula 10 da kuma Dark. Akwai wasu kuma daban.

 

Wane amfanin kitso yake ga mace?

Amfanin kitso ga mace yana da yawa, har yanzu al’adar nan ta aika wa neman yardar makitsiya da samun lokacin yin kitson tana nan. Magidanta mafi yawansu na bai wa kitson matansu muhimmanci. Kitso alama ce ta tsabta domin yana  sa  kamshin kai domin man da aka yi kitson da shi. Kuma gashin na kyau domin an gyara shi, sannan ya kara wa mata kyau wanda hakan ke kara dankon soyayya.

 

Me rashin yin kitso ke sanyawa ga mata?

Da zarar mace ba ta kitso ai daga nan matsala ta fara, gashin kai na daga cikin sassan jiki masu bayyana wari ga mutum, musamman mata. Rashin yin kitso na haddasa matsaloli kamar lalacewar gashi da sauransu.

 

Kamar tsawon lokaci ne ya kamata a yi kitso?

Ya zama tsakanin kwana goma zuwa mako biyu, in son samu ne kada ya wuce haka.

 

Me ke sa mata son yin kitson Sallah? 

Duk Bahaushiya na son yin kitso domin bikin Sallah, kasancewar lokaci ne na kawa da nuna sutura.

 

Kin dauki kitso sana’a ce ko kawai sha’awa kike? 

Gaskiya kitso sana’a ce a wurina, domin ni dai na yi duk ’yan abubawa da nake son in yi da kitso. Za ki san mutane daban-daban, kama daga ’yan mata da ma’aurata da ma’aikatan gwamnati har da wadanda ba ki yi tsammani ba. Idan kuma ba ki yi hankali ba akwai ’yan matsaloli domin za ki hadu da matsalolin mata daban-daban, wani lokaci zai kasance kishiyoyi biyu ko sama da haka duk a wurinki suke kitso, matukar ba ki yi hankali ba akwai kura, domin kowace za ta zo miki da nata sirrin.

 

Ta yaya ake koyon kitso?

Gaskiya ban tunanin ana koyon kitso a fahimta. Wannan baiwa ce daga Allah domin ban taba ganin an je da wadansu da sunan ana koya musu kitso ba, ko a ce ga wani lokaci da aka diba domin koyonsa. Abin da na sani yawan kallon yadda ake yi zai kara sa ki kware, domin za ki  ga nau’o’in kitson.

Na san dai a wajen gyaran gashi na zamani wato (saloon) akan dauki lokaci mace na ganin yadda ake wanke gashi da sanya shi bushewa kafin a yi kitson kawai.

 

A yini mace nawa kike iya yi wa kitso?

Ya danganta daga wane iri kitso za a yi ko ya yawan gashin wacce za a yi wa kitson. Misali idan amarya ce, dole kitson zai dauki lokaci domin dole a fito da ita sosai.

 

Kina fuskantar matsaloli?

Kamar yadda na bayyana ne a baya, sai kuma kasancewar halin da muke ciki a yanzu na bazuwar cututtuka a cikin al’umma wadanda suka sa mafi yawan masu zuwa kitso sun fi son zuwa da tsinke da matajinsu, domin kiyaye amfani da na wani.

Sai kuma gwamnati  ba ta cika daukar sana’ar kitso a matsayin sana’ar da za a sanya a cikin jerin kananan sana’o’in hannu ba. Wannan na daga ciki matsalolin da sana’ar kitso ke fuskanta a halin yanzu.

 

A fannin nasarorin da kika samu fa?

Gaskiya akwai samun kudi. Babbar nasarar wannan sana’a ba kamar zumunta kasancewar mu mata muna da saurin kulla zumunta. Akwai mutane da yawa da wannan sana’a ta sanya sun zama kawaye  da ’yan uwantaka ta kut-da-kut.