✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar dinki ta taimaka wa karatun da nake yi a jami’a -Hamza Adam

Wani matashi mai suna Hamza Adam da yake sana’ar dinki a Legas ya ce ba don sana’ar ba da yanzu ba ya karatu a jami’a.Ya…

Wani matashi mai suna Hamza Adam da yake sana’ar dinki a Legas ya ce ba don sana’ar ba da yanzu ba ya karatu a jami’a.
Ya ce, rashin samun isassun kudin da zai dauki nauyin karatun bokon da yake yi, ya sa ya rungumi sana’arsa ta dinki gadan-gadan.
Hamza, wanda dan asalin garin Jos ne a Jihar Filato, wanda kuma yake aji uku a tsangayar ilimin koyon aikin injiniya a Jami’ar Maiduguri ya shaida wa Aminiya, a wata tattaunawa da ta yi da shi, cewa burinsa shi ne ya kammala karatunsa na boko. “Sana’ar dinki ta taimaka mini sosai kan wannan fannin. Burina in samu in kammala karatuna na boko, shi ya sa nake amfani da abin da nake samu a sana’ata ta dinki, duk da ina da kalubalen rashin isassun kudin daukar dawainiyar karatun nawa, musamman ma dayake ba ni da wanda zai dauki nauyina wajen biyan kudin makaranta”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa duk da matsalolion da yake fuskanta, yana da yakinin cewa Allah Zai taimaka masa ya cimma burinsa na zama kwararren injiniya, wanda zai taimaki al’umma.
Hamza, mai kimanin shekara 29, ya bayyana cewa tun yana aji daya a sakandare ya fara daukar dawainiyar karatunsa sakamakon mutuwar mahaifinsa.
Wani al’amari da ya sa ya kama sana’ar dinki shi ne kari da sha’awar ya zama tela. “Tun ina karami nake sha’awar koyon dinki, amma mahaifina sai ya ki barina, saboda ya fi son na yi karatu. Bayan da ya rasu ne, sai na kai kaina wurin da ake dinki, inda na koya, sannan sai na ga ya dace na koma makaranta. Na samu na koma din kuma na rika biyan kudin makaranta da kaina, har na gama karatun sakandare. Daga nan na sami nasarar shiga Jami’ar Maiduguri, sashen koyon ilimin injiya. Saboda haka ni ban yarda da cewa idan ba ka da wanda zai dauki nauyi karatunka ba za ka iya karatu ba. Idan mutum yana da wannan ra’ayi ya zama ragon-maza. Saboda haka duk abin da ka sa a gaba, in dai na alheri ne, Allah Zai taimake ka”. Inji shi.
Daga nan sai ya bayyana cewa ci gaba da karatun boko na daya daga cikin nasarorin da ya samu a sana’ar dinki.
Ya bayyana cewa ya sha wahala kwarai da gaske a lokacin da yake koyan sana’ar dinki don sau biyu yakan ci abinci a rana.
Don haka sai ya ce hakuri da juriya su ne sirrin da ya sa ya sami nasarar hada sana’ar dinki da karatun boko. Amma ya ce idan yana makaranta ba ya yin sana’ar dinki, har sai ya sami hutu saboda kada sana’ar dinkin ta dauke masa hankali daga karatun da yake yi.
Ya shawarci matasa su tashi tsaye don cimma burin da suka sa a gaba. “Babu abin da ba za ka iya zama ba, amma ya danganta da yadda ka dauki kanka. Idan ka dauka komai za ka iya, to Allah Zai taimake ka. Idan kuwa ka dauka ba za ka iya komai ba, to za ka rika komawa baya”. Inji shi.