Akalla mutum shida ne suka rasu sakamakon kamuwa da cutar sanƙarau a Kananan Hukumomin Nafada da Funakaye a Jihar Gombe.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Habu Dahiru ne, ya sanar da haka da yammacin ranar Alhamis.
- An cafke wata mata kan sayan jaririyar wata 3 a Ekiti
- An maka Alƙali a Kotu kan rushe gidan marayu a Zariya
Ya ce hukumar lafiya ta jihar ta gudanar da bincike tare da tabbatar da bullar cutar a kananan hukumomin biyu.
Ya ce an tabbatar da mutuwar mutum shida; mutum biyar a Karamar Hukumar Nafada, yayin da wani mutum daya ya rasu a Karamar Hukumar Funakaye.
A cewarsa sun samu rahoton bullar cutar ne a ranar 18 ga watan Fabrairu 2024, bayan yi es mutum 95 gwajin cutar a Babban Asibitin Garin Funakaye.
A cewar Kwamishinan, an sallami mutum 84 daga cikin mutum 95 da suka kamu da cutar, yayin da mutum shida ke ci gaba da karbar magani a asibiti.
Ya kara da cewar daga cikin wasu mutum 29 da aka yi gwaji, an samu mutum biyu dauke da cutar.
Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayar da umarnin bayar da magunguna da tallafi ga asibitin don domin dakile yaduwar cutar.
Gwamnan ya umarci farfado da Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) a jihar.
Ya yi kira ga jama’ar jihar da kaucewa kwanciya cikin zafi da kuma cunkoso domin hakan na iya haifar da cutar sanƙarau.