Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa, sun yaba wa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, bisa bai wa Nasir Bala Ja’o’ji muƙami a Majalisar Zartaswa ta Babbar Kwalejin Ilimi da Fasaha ta Tarayya, Potiskum, da ke Jihar Yobe.
A wata wasiƙar taya murna da shugaban shiyyar ƙungiyar, Makama Dan Kaduna, ya sanya wa hannu bayan wani taro da suka gudanar a Kaduna, sun ce Ja’o’ji mutum ne mai kishin matasa da ƙoƙarin inganta rayuwarsu.
Sun bayyana cewa, “Wannan muƙami da Sarkin Daura zai ba shi, ya ƙara tabbatar da binciken da muka gudanar wanda ya nuna cewa Ja’o’ji yana cikin shugabannin matasa 10 da suka fi fice da kwarjini a jihohin Arewa.”
Ƙungiyar ta kuma jinjina wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, bisa ƙoƙarinsa wajen inganta rayuwar matasa.
Sun ce, “Nan ba da jimawa ba za mu fitar da sakamakon bincikenmu wanda ya gano 10 ciki har da Nasir Bala Ja’o’ji, da suka yi fice wajen tallafa wa matasa a Arewa. Za mu karrama su ɗaya bayan ɗaya.”
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu.
“Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.”
Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura.
“Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.”