Daya daga cikin manema takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sanata Ahmad Rufa’i Sani Yarima, ya ce samar da Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinai za ta taimaka wajen inganta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai a kasar.
Tsohon gwamnan Jihar Zamfaran ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Shugaban Gidauniyar Zaman Lafiya kuma Babban Limamin Cocin San Saturino, John Cardinal O. Onaiyekan a Abuja.
- ISWAP ta kashe wani Babban Kwamandan Boko Haram a Borno
- Mun daina kai wa CBN ajiyar kayan zabe —INEC
Ziyayar dai na zuwa ne a matsayin wani bangare na shawagin tuntube da neman shawarwari da Sanata Yarima ke gudanarwa domin cimma burinsa na zama shugaban kasar Najeriya a babban zaben 2023 da ke tafe.
Sanata Yarima ya yaba wa babban limamin bisa addu’o’in da yake yi wa kasar nan na inganta zaman lafiya da kuma tabbatar da hadin kan al’ummarta.
Yariman Bakura ya kuma tabbatar wa limaman cocin cewa duk da cewa manufarsa ita ce ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a ciki a yanzu, zai kuma kasance mai biyayya ga jam’iyyarsu APC kuma mai mara wa duk dan takarar da jam’iyyar za ta tsayar idan har bai samu tikitin jam’iyyar ba.
Sanata Yerima ya ce “Na kawo kaina domin sanar da kai cewa ina cikin masu neman shugabancin kasar nan da kuma neman addu’a da goyon bayanka.
“Ina bukatar addu’o’i daga kungiyoyin addinai daban-daban musamman daga limamai irinka, domin neman yardar ’yan Najeriya zuwa ga shugabanci nagari.
“Wannan shi ne karo na biyu da na ziyarce ka, amma ziyarata ta yanzu na zo ne domin neman addu’o’inku kuma ina fatan zan sake dawowa karo na uku domin neman karin addu’o’i da kuma samun tabarraki.”
Da yake jawabi, Mai Martaba John Cardinal Onaiyekan, ya ce ana son dan Adam ya yi iya kokarinsa amma Allah ne kadai ya san abin da zai faru gobe da wadanda za su jagoranci Najeriya.