Sama da matasa 300 ne suka amfana da ayyukan taimako da wata kungiya da ke zaman kanta da ake kira Majalisar Macccido da ke garin Andaha a karamar Hukumar Akwanga na Jihar Nasarawa ke yi wa al’ummomin kankara a bara. Shugaban kungiyar, alhaji Adamu Tanko ne ya sanar da haka a jawabinsa a wajen taron bude sabuwar sakatariyar kungiyar da taron kunkiyar na karshen shekara da aka gudanar a garin Andaha rana.
Shugaban ya ce baya ga taimako da tallafi da kungiyar ke bai wa matasa da sauran marasa galihu, ta gina tare da kaddamar da asibitoci da makarantu da dama a yankin karamar Hukumar Akwanga baki daya, musamman a kauyuka, sannan ya bayyana cewa nan bada dadewa ba kungiyar za ta gina wani katafaren dakin taro a garin Andaha inda hedikwatarta take tare da ci gaba da samar wa al’ummar yankin abubuwan more rayuwa musamman a bangaren kiwon lafiya da ilmi da sauransu don tallafa wa kokarin gwamanati.
“Ina so in sanar da ku cewa kungiyar Majalisar Maccido za ta shiga sabuwar shekarar 2018 ne da sababbin akidun samar wa al’ummominmu musamman wadanda ke karkara abubuwan more rayuwa kamar yadda take yi ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba domin rage wahala da matsalolin.”
A na shi bangaren, shugaban taron alhaji Adams Alhassan Doma wanda shi ne mai taimaka wa Gwamnan Jihar a kan harkokin kungiyoyi ya bayyana kungiya a matsayin mahimmin hanyan taimakon al’umma musamman mazauna karkara. Ya ce makasudin kafa kungiya shi ne don samar wa al’umma musamman marasa galihu abubuwan jin dadin rayuwa kamar yadda a cewarsa kungiyar Majalisar Maccido take yi, sannan ya bayyana cewa ayyukan kungiyar yana da dangantaka da yakin neman ‘yanci da kiwon lafiya da tabbatar da cigaba a yankunan karkara. Ya ce ba shakka ayyukan kungiyar wacce a cewarsa ba ta samun tallafi daga wani wuri yana dai dai da manufofin gwamnatin APC a jihar karkashin jagorancin Gwamna Umaru Tanko Almakura, sannan ya tabbatar wa kungiyar cewa zai sanar da gwamna Almakura dukan abubuwan cigaban da da kungiyar ke aiwatar don gwamnati ta tallafa musu don su samu damar cigaba da gudanar da wadannan ayukan. Sauran abubuwa da aka gudanar a wajen taron sun hada da raba wa mata da yara da nakasassu kyaututtuka da suka hada da zanuwa da kayayyakin abinci da sauransu.