✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sam ba da Nafisa nake maganar tarbiyya ba – Sarkin Waka

Naziru ya ce sam bai kama sunan Kannywood ba, masana’antar fim kawai ya ce

Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan wata muhawara da ta barke a masana’antar Kannywood kan batun tarbiyya, tsakanin mawaki Naziru M. Ahmad da jaruma Nafisa Abdullahi, mawakin ya ce sam ba da jarumar yake ba.

Mutane da dama sun yi ta fashin bakin cewa kalaman Nazirun, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka gugar zana ne ga Nafisan.

Sai dai bayan lamarin ya dauki zafi, Naziru ya ce shi ba da Nafisat yake yi a wani sakon murya da ya aika da Aminiya ta samu.

A muryar, an jiyo shi yana cewa, “Ni ban ce Kannywood ba, babu ruwana da ita. Masana’antar fim na ce. Duniya ke nan.

“Kuma duk misalin da na yi, duk wanda yake cikin masana’antar ya san gaskiyar maganar, ya san wadanda suka yi daidai da hakan.

“Kuma wallahi na rantse da Allah ka ga azumi ake yi ba da Nafisa nake yi ba. Wasu na gani a tiwita suna rubutu.”

Sai dai da Nazairu ya samu labarin muryar ta fita, ya saki wani bidiyon inda ya ce wanda ya saki muryar, duk da cewa bai fita sosai ba, ya ci amanarsa.