✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauya ministoci: Tinubu ya rushe wasu ma’aikatu, ya haɗe wasu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rushe ma'aikatun kula da yankunan Arewa da Kudu.

A wani bangare na sauya majalisar ministocinsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rushe Ma’aikatar Bunƙasa Ci-gaba Arewa da takwarorinta na sauran yankuna.

Kakakin Shugaban kasa,  Bayo Onanuga ya ce Majalisar Zartaswa ta Kasa ta kuma amince da rushe Ma’aikatar Bunƙasa Ci-gaban Wasanni tare da mayar da ayyukanta ƙarƙashin Hukumar Kula da Harkokin Wasanni.

Onanuga ya kara da cewa an rushe Ma’aikatar Bunƙasa Ci-gaban Neja Delta da Ma’aikatar Bunƙasa Ci-gaban Kudu maso Gabas.

Ya bayyana cewa za a kafa sabuwar hukumar bunƙasa Ci-gaban Yankuna, wadda za ta ci-gaba da jan ragamar ayyukan ma’aikatun yankunan.