✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah Karama: Ganduje ya ba ’yan makaranta hutu

Hutun zai fara daga ranar Talata zuwa Litinin.

Gwamnatin Jihar Kano ta ba wa dalibai hutun Karamar Sallah da ake shirin gudanarwa a mako mai zuwa.

Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin ilimi, Jilani Almustapha Danmalam ne ya sanar da ranar hutun.

Hutun zai fara ranar Talata 11 zuwa Litinin 17, ga watan Mayu.

Sanarwa ta bukaci iyayen dalibai da su ba tabbatar yaran sun koma makaranta a ranar da aka sanya ta komawa makarantu.