Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Kaura-Namoda/Birnin-Magaji, Aminu Jaji, ya sayi raguna 3000 don raba wa jama’ar mazaɓarsa da kuma ‘ya’yan jami’yyar APC a Jihar Zamfara.
Ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin gudanarwar Jaji, Aliyu Abubakar, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.
- ’Yan sanda sun kama ɓarayi 6, sun ƙwato motoci 5 a Kaduna
- Kansila ya ɗauki nauyin karatun marayu 120 a Kano
A cewar sanarwar, Jaji ya kuma ware Naira miliyan 250 don raba wa mutane, marayu, da ƙungiyoyin agaji a faɗin jihar, don gudanar da bikin sallah cikin walwala.
“Wannan wata dama ce da ke zuwa shekara-shekara da nufin taimaka wa musulmi, musamman ’yan jam’iyyar APC da marasa ƙarfi, don yin bikin sallah cikin walwala.
“Waɗanda za su amfana da wannan taimako sun haɗa da ƙananan hukumomi, da shugabannin jam’iyya da dattawan jam’iyya da tsofaffin masu riƙe da muƙaman siyasa.
“Sauran waɗanda za su amfana sun haɗa da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi, mataimakansu, tsofaffin ’yan majalisa da kuma ƙungiyoyin APC da sauransu.
“Akwai malaman addinin Musulunci, marayu, matasa da mata masu tallafa wa jam’iyyar APC da sauransu,” in ji sanarwar.
Jaji ya yi kira ga Musulmi da su ƙara ƙaimi wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.