✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Salihu Tanko Yakasai yana hannu —DSS

Muna bincike ne a kan batutuwan da suka wuce na bayyana ra’ayi.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta tabbatar da kame Salihu Tanko Yakasai, wanda ke zaman tsohon mai magana da yawun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano a kafofin sadarwa na zamani.

An yi ta ce-ce-ku-ce kan inda tsohon hadimin gwamnan ya shiga tun bayan da aka neme shi aka rasa daga yammacin ranar Juma’a har zuwa wayewar garin Asabar.

Mahaifin Salihu, daya daga cikin Dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya tabbatar wa da Aminiya cewa wasu jami’an tsaro ne suka kama dan nasa bayan ya fita da yammacin ranar Juma’a.

Ma’abota dandalan sada zumunta musamman Twitter da Facebook sun yi ta tayar da kura a kan cewa an kama Salihu ne wanda aka fi sani da Dawisu saboda sukar gwamnatin jam’iyyar APC a dukkan matakai da cewa ta gaza sauke mafi girman nauyi da rataya a wuyanta na tsare rayukan al’umma.

Sai dai a wata sanarwa da Kakakin Hukumar DSS Peter Afunanya ya fitar a yammacin ranar Asabar, ya ce tabbas tsohon hadimin gwamnan yana hannunsu kuma ana gudanar da bincike a kansa.

“Wannan sanarwa na tabbatar da cewa Salihu Tanko Yakasai yana hannun Hukumar DSS kuma ana gudanar da bincike a kan batutuwan da suka wuce na bayyana ra’ayi a kafafen sada zumunta kamar yadda wasu jama’a ke zargi,” inji Afunanya.

Dawisu a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a bayan rahoton sace dalibai mata fiye da 300 a Makarantar GGSS Jangebe da ke Jihar Zamfara, a ce gwamnatin APC ta gaza kuma mafi a’ala shi ne ta yi murabus.

Sai dai a lokacin da Salihu ya wallafa wannan sako yana zaman hadimin Gwamna Ganduje, kuma bai kebance kansa daga wannan gazawa ba, duba da shi a kansa jami’in gwamnatin APC ne a Jihar Kano.

A dalilin haka ne gwamnatin Jihar ta bakin Kwamishinan Labarai, Muhammad Garba, ta sanar da sauke shi daga mukaminsa a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar kan sukar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Garba ya ce sallamar wacce ta fara aiki nan take na zuwa ne sakamakon yadda Salihu kasancewarsa jami’in gwamnati yake ci gaba da furta lafuzan da suka sha bamban da na matsayin gwamnatin da yake yi wa wakilci.

Aminiya ta ruwaito cewa, a daren ranar Juma’a ne ’yan bindiga suka kai hari makarantar mata zalla ta Jangebe da ke Karamar Hukumar Talata Mafara a Jihar Zamfara, inda suka wawushe dalibai fiye da 300 wanda a halin yanzu an tabbatar suna tsare a Dajin Dangulbi da ke Karamar Hukamar Maru ta Jihar.