Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ɗan wasan gaban kungiyar Mohamed Salah zai ci gaba da zama duk da sabbin rade-raɗin da ake yi cewa zai koma buga gasar ‘Saudi Pro League’.
An ruwaito cewa Al-Ittihad na zawarcin dan wasan gaban na Kasar Masar mai shekara 31, wanda ya koma Liverpool daga Roma a shekarar 2017.
- Mun kakkabo jirage marasa matuka 42 daga Ukraine —Rasha
- Yadda ake jana’izar sojojin da ‘yan ta’adda suka kashe
Da yake magana gabanin wasan da Liverpool za ta buga da Newcastle a ranar Lahadi mai zuwa, Klopp ya ce Salah ya jajirce dari bisa dari ga kungiyar.
Liverpool ba ta son sayar da dan wasan wanda da ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya ta shekaru uku a bazarar da ta gabata kuma za a rufe kasuwar musayar ’yan wasa a ranar 1 ga Satumba.
Salah ya fara buga wasanni biyu na Liverpool a kakar wasa ta bana, duk da cewa ya nuna rashin jin dadin yadda aka sauya shi a wasan da suka tashi kunnen doki da Chelsea, kafin ya ci kwallo daya a wasan da kungiyar ta doke Bournemouth.
Ya zura kwallaye 187 a wasanni 307da ya yi wa Liverpool kuma ya lashe Gasar Zakarun Turai da Firimiyar Ingila da FA Cup da League Cup da FIFA Club World Cup da kuma UEFA Super Cup a Anfield.