✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka yi jana’izar sojojin da ‘yan ta’adda suka kashe

Janaz'izar na gudana ne a Makabartar Sojoji da ke Abuja.

Rundunar sojin Najeriya ta fara gudanar da Jana’izar Soji ga dakaruta da ’yan ta’adda suka hallaka.

Janaz’izar na gudana ne a Makabartar Sojoji da ke Abuja sakamakon rasuwar sojoji 20 a yayin musayar wuta da ’yan bindigar da suka kai musu hari a Jihar Neja a makon jiya.

A makon jiya kadai rundunar tsaron Najeriya ta rasa mutum 36 daga cikin dakarunta a Jihar Neja.

Da farko sojoji 22 ne rundunar ta tabbar da rasuwarsu a harin kwanton ɓauna a kan hanyar Zungeru-Tegina da ke jihar.

Daga bisani wasu 14 suka kwanta dama a hatsarin jirgin soji a yankin Chukuba da ke Karamar Hukumar Shiroro.

Ministan Tsaro Muhammad Badaru Abubakar da Mataimakinsa Bello Mohammed Matawalle da manyan hafsoshin tsaro, da gwamnoni, sun halarci taron jana’izar.

’Yan siyasa da jami’an gwamnati da iyalan mamatan da kuma abokan arziki da na aiki na daga cikin mahalarta taron jana’izar sojojin.

Wannan shi ne adadi mafi yawa na sojojin Najeriya da suka rasu a sakamakon harin ’yan ta’dda a baya-bayan nan.

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta lashi takobin dandana wa duk wanda ya taba dakarunta kudarsa.