Kira ga Gwamnoni
Gwamnonin Najeriya ya kamata ku kara azama sosai wajen samar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’ummominku, musamman ganin yadda dimbin al’umma suke cikin kuncin rayuwa.
Daga Haruna Muhammad Katsina. Shugaban kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina.07039205659 [email protected]
A yi koyi da Gwamna Masari
Zuwa ga Edita, hakika Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ka yi wa matasa yadda ake yi, domin dauko matashi irin Hamza Suleman Faskari da ka yi ka saka cikin gwamnatinka a matsayin Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, ya nuna cewa, lallai ka cika dattijo. Domin saka irin su Hamza Suleman Faskari da ka yi ya zame wa matasan Faskari abin mamaki ganin yadda yake taimaka wa mutane da ayyukkan yi, wanda hakan ne ya kamata kowane Gwamna ya dinga yi wa mutane domin samun daidaito ga kowa. Saboda haka muna yi wa Gwaman Masari addu’ar Allah Ya yi maka jagora a cikin mulkin ka tare da gamawa lafiya da kowa.
Daga Usman Adamu Aliero Jihar Kebbi, [email protected] 07061594299.
Ga Sambo Dasuki
To, Sambo Dasuki ai duk tsuntsun da ya kira ruwa shi ruwa kan doka. Fatanmu dai Allah Ya sa hukumar tsaron Najeriya za ya yi masa hukunci daidai da laifin da ake zarginsa da shi.
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999 [email protected].
Ta’aziyyar mutanen Bam
Assalamu alaikum, Aminiya mai farin jini ku ba ni dama in mika sakon ta’aziyyata zuwa ga ‘yan uwa da iyalan al’ummar garin Bam, da ke karamar Hukumar Biu, da ke Kudancin Jihar Barno sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da ya lakume rayukan akalla mutum da kuma raunata sama da mutum 30. A gaskiya wannan abin alhini ne kwarai da gaske idan aka yi la’akari da irin zullumin da al’ummar wannan yanki ke fama da ita. Da wannan muke kira ga sojojin Najeriya da su kara azama wajen ganin sun ceto ‘yan matan da aka sace a makarantar ‘yan mata da ke garin Konduga, da ‘yan matan makarantar garin Chibok, da kuma na wanda aka sace a kauyen Bam, da ke kudancin jihar Borno. A karshe muna addu’ar Allah Ya kawo mana karshen ayyukan masu tada kayar baya da ke lakume rayukan al’ummar Arewa, da ma sauran sassan kasar mu Najeriya baki daya amin.
Daga Adamu Aliyu Ngulde, 08032135939. dalibi A Sashin Koyon aikin Jarida da ke Jami’ar Maiduguri.
Kira ga Gwamna Masari
Haba Gwamnatin Jihar Katsina, a gaskiya ya kamata ku tausaya wa Malaman makarantun Firamare, domin kuwa sama da wata shida ke nan amma kun kasa biyan albashin malamai, duk da muhimmancin da suke da shi, a wannan jiha tamu. Saboda haka ya zama wajibi ga Gwamna Aminu Bello Masari da ya yi gaggawar duba wannan matsala, ganin irin yadda Malaman suka samu kansu a ciki na mawuyacin hali na fatara da talauci, kuma tabbas hakan ba zai ba su karfin zuwa makarantun ba a kowane lokaci domin karantar da dalibai ba.
Daga Sanin Shaga kofar kaura Katsina. Jami’in Hulda da jama’a na kungiyar Muryar Talaka, reshen Jihar Katsina, [email protected].
Gaisuwa ga aminai
Gaisuwa da fatan alheri a gareku baki daya. Da fatan kuna lafiya. Allah ya sa haka ameen.
[email protected]
Kira ga Gwamna Ganduje
Aminiya ku taimaka min ku gaya wa Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam, ya taimaka ya gyara gadar Kubaraci, hanyar Kura zuwa Madobi. Mutanen wajen a yanzu babu wani abu za a yis musu da ya wuce wannan aikin.
Daga 09093333955 Agege Jihar Legas. Rabi’u Yunus [email protected].
Ta’aziyyar danwanzan
Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un, ko shakka babu dukkan mai rai mamaci ne. A yau Edita ina son ka ba ni dama in mika sakon ta’aziya ga iyalai da abokkan arziki na marigayi Alhaji Muhammadu danmalam, wanda muka fi sani da danwanzam, da Allah ya yi wa cikawa a ranar Jumu’a 27-11-2015.
Tabbas wannan babban rashi ne, ba ga iyalansa kadai ba, har ma ga dukkanin Hausawan duniya, in an yi la’akkari da yadda wannan dan tahaliki ya ba da gudumuwarsa matuka, a lokacin da yake raye wajen yada harshen Hausa, ta hanyar sana’arsa ta wasan kwaikwayo. Muna rokon Allah Ya jikansa, Ya sa aljanna firdausi ce a makomarsa.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu, Gusau (Sarkin Hausawan C.o.e Maru)08069807496 [email protected].