✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonnin Dalibai

A wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintaccciyar jaridar kasar haurobiya, mun baje muku sakonnin ‘’yan makaranta. A shakaratu lumui sumul kalau: A daina…


A wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintaccciyar jaridar kasar haurobiya, mun baje muku sakonnin ‘’yan makaranta. A shakaratu lumui sumul kalau:


A daina wulakanta Hauro

Bayan Sallama irin ta addinin gaskiya. Ina fatan dukkan dalibai da masu makalewa (‘yan kulallabo-kulabe) a kan katanga su na leke da satar kallon abin da ake yi a makaranta, ina fatan dai duk muna amfana da karatun da shehin shehinnan wannan makaranta kuma direban alli yake bayarwa ba tare da muna ba shi ko na na-tulu ba.

Ina kira ga jama’armu ta Haurobiya da mu kiyayi wulakanta damin hauro, wannan abu yana ci min tuwo a akushi, idan na ga yadda jama’a ke dukunkunawa da yaga damin Hauro, musamman masu sana’a ba sa shiryasu yadda ya kamata. Da an ba su sai su cimimiyesu, su saka aljihu ko jaka, sai ka ga Hauron leda duk ya lalace ya kone ka rasa yadda ake yi ya zama haka.


Da fatan za mu gyara.

Ina yi wa shehin shehinnan wannan makaranta kuma direban alli Farfesun ilimi fatanmu Mai-ni-da-kai, Mahaliccin sammai da kassai ya yi masa jagoranci akan dukkan rayuwarsa, tare da hukumar kamfanin Amintacciyar Jaridar da suka bayar da wannan dama ta ilimantarwa.

Na gode. Umar M. Abdullahi (Faruk Gwammaja) 08067676454, 08099767645


Godiya ga ’yan makaranta

Sallama a gare ku daliban wannan makaranta da masu zuwa leke da daukar karatu ba tare da mun sani ba, muna yi muku godiya kuma muna fatan alheri a gareku.

Kamar yadda aka sani dai ga ‘yan kungiyar da mai sha’awar zama daya daga cikin ‘yan kungiyar wannan makaranta na reshen Jihar Tumbin Giwa mai iyaka da Ta-Dikko dakin kara da Jihar Jijjiga-ciyawa, da ma kasar Haurobiya muna nan muna shirin kiran taro, ana iya neman mu ta lambobin kurtun maganarmu: Mal. Aliyu Mukhtar Sa’id (IT) – 08034332200, Umar M. Abdullahi – 08067676454.

[email protected], [email protected] Mun Gode


Takaddamar Gwamna Kadoji da direbobin alli

Assalamu Alaikum. Jama’a barka da warhaka, da fatan kowa yana cikin koshin uwar jiki. Zan yi amfani da wannan kishiyar hagu na isar da gaisuwata, sannan kuma na yi karin bayani dangane da batun da Gwamnan Jihar Kadoji ya yi na sallamar direbobin allin ‘yan dugwi-dugwi, sakamakon samun wasunsu da rashin cancantar zama direbobin allin, duk da an ce sun sha inuwar sili, illa iyaka dai kamar ba su koyi abin da ya kamata su koya ba a lokacin da direbobin suke koyar da su, ko kuma ma alfarma ce ta kawo su aikin.

Na tuna wani lokaci da na taba zama direban alli a shekarar dubu karamin lauje da karamn lauje (2002) a wata makaranta a matsayin malamin lissafi, duk da cewa ni Islamiyya na yi, a wannan makarantar akwai wani malami da yake koyar da Labarci, ya shiga aji tsayuwa da kafa daya (4), ya gama karatu, sai wani ya ce, “malam an ce sunayen doki suna da yawa, Hisanun da Khailun duk sunan sa ne” sai ya ce wa yaran babu wani suna da doki yake da shi in ba Farsun ba.

Na shiga ajin zan yi karatu, sai wani yaro ya ce an ce musu wai na iya Larabci, ya sunan doki da Larabci, na yi dariya na ce, sunayen doki suna da yawa, na fada musu wadan da na sa ni, sai na ji ana ta dariya da surutu kasa-kasa, da na tambaya aka ce malam wane ya ce doki suna daya gare shi a Larabci. 

Da na ji haka, sai na ce musu, ina tsammanin malam ba ya son ku rike abin da ba shi ya koya muku ba, shi ya sa ya barku a kan wannan sunan.  Sai na ji suna cewa an ce fa dama ko firamare bai gama ba.

Bayan na fito na sami malamin na sanar da shi yara sun tambaye ni sunan doki na ce Hisanun, sun ce wai ka ce babu wani sunan doki in ba Farsun ba, sai ya ce “akwai ke nan?” Na ce kwarai kuwa, sai ya ce “ni fa kullum idan an tashi daga nan na ke zuwa wajen abokina ya koya min abin da zan yi gobe, shi ke nan sai ka rika koya min a nan ofis” ya  ce “to me ka ce musu?” na ce, “ina tsammanin don kar ku rike abin da ba ba shi ya koya muku ba ne”.

Shi da kan sa yake ba ni labarin alfarma aka yi masa na samun aikin koyarwa daga karamar hukuma, bayan gadon da aka ba shi na mahaifinsu (wani mai kudi ne a Jihar Tumbin-giwa) ya lalace aka nemar masa koyarwa, alhali shi bai yi karatu mai zurfi ba.

Shawarata ga Gwamna shi ne, Ina ga ya maimakon sallama ya kamata a ce wajen aikin aka sake wa wadannan malamai, domin matsala za a samu mai tarin yawa idan har aka sallame su.

Daga cikin matsalan akwai bara da roke-roke da sake-sake da cuta da neman kudi ta kowace hanya.

Allah ya kare. Na gode, Umar M. Abdullahi (Faruk Gwammaja) 08067676454, 08099767645


Dodannin Bokoko

Cikin hikima da natsuwa da sanin ya kamata, Amintacciyar jarida mai albarka mai dauke da tsararren shafin makarantar Dodannin Bokoko, jinjina da ban-girma ga jagaba Dodo duk da shehunan malamai da mu ‘yan talazaiyen dalibbai mun zura na mujiya tare da fashin bakin fassara Hausa a cikin Hausar fasaha (hausar husaha). karin godiya ga silar lalubo mana wannan shafin Shehin Malami B.B. Usman a Jami’ar Shehu danfodiyo da ke Sakkwato. Mun gode Daga 

Halliru Barau Dankawu, 

Birnin Shehu (Wazirin Hausawan UDUSOK amma mai Garin-Gado) 07032545969, 0803331339.


Dodanni a isar da sako

Dodannin albarka ku isar min da sakon godiya ga Sanatan Gobirawa na gudummawar da yake ba da wa a fannin ilmin Sakkwato ta Gabas. Kuma ku mika min gaisuwa ta ga Umar Mukhtar Kano bisa gudunmawarsa ga wannan fili mai albarka tare da Shugaban rundununar adalci na Sakkwato Bashar Altine Isa. Allah ya taimaki Sardaunan Gobir, Sanatan yau da gobe da yardar Allah.

Daga Aminu Galadima Isa Sokoto Birnin Shehu

Jiki Magayi Isa Chapter 

07032883333


Jinjina ga Dodo

Barkanmu da warhaka. Ina mika jinjina da gaisuwa ta ga mai gabatar da wannan shafi na Dodorido, bisa irin yadda yake fadakarwa cikin hikima da salon Hausa, ba tare da cin mutuncin kowa ba. Haka nan ma ina yi wa kamfanin da ke samar da Jaridar ta Hausa mai albarka, da fatan Allah ya daukaka dukkan ma’aikatanta, ya yi musu jagoranci, Amin.

Na gode Amina (kueen)

Bayan Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Jihar Tumbin Giwa (Kano)


Jinjina ga jagoran jujjuya jumla

 Assalamu alaikum. Allah Ya kara wa malam sani, amin.

A farko-farkon mulmulowar Aminiya, na dauki dandalin Dodorido a matsayin wani dandamali na dabaibayin daburtar da marena Hausa kurum. Amma da nis soma suntubawa, bayan na sarrafa Sakkwatancina, sai na soma sunsuno salailan wannan masani, wato Dodorido. daya daga cikin masu hazaka a Haurobiya. 

Ka ci gaba da fasalta fasaharka. Ni dai zan ci gaba da tu’ammali da tarihi, a yayin da nake hwashin bakin Hausa a Haurobiya, wai ni Basakkwace, dan Yabo, garin Moyijo.


Bari in ja da baya, in kama bakina, kada in cika ka da surutu daga nan Sakkwato. Amma kafin in kammala, sai na sake jinjina wa wannan jagora na jirkita jumla, ba tare da bukatar a jinjina ma ni ba.

 N a gode.  Akilu M. Shehu Yabo, Haujin Birnin Shehu. Haurobiya. (07088213989),   [email protected]/