Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ba wa mai dakin shugaban kasa, Remi Tinubu, sako ta sanar da mijinta cewa al’ummar Najeriyar na cikin halin kaka-ni-ka-yi, saboda haka ya yi abin da ya dace.
Sarki Aminu Ado Bayero ya kuma bukaci Tinubu da ya sake tunani kan shirinsa na dauke Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAN) da kuma sasan Babban Bankin Najeriya (CBN) daga Abuja zuwa Legas.
Sarkin ya ba wa Remi Tinubu sakonnin ne a lokacin ziyarar ban-girma da ta kai masa fadarsa da ke birnin Kano a safiyar Litinin.
Ga jerin sakonnin nasa:
1- Al’amura sun yi tsauri, kayan abinci sun yi tsada, mutane ne cikin wahala.
2- Ma’tsalar tsaro na ci gaba da addabar jama’a don haka ya kamata a magance ta.
3 – A sake tunani kan shirin dauke Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman (FAAN) da kuma Sassan Babban Bankin Najeria (CBN) daga Abuja zuwa Legas.
Sarkin Kano ya jaddada bukatar Gwamnatin Tinubu ta kawo wa talakawa dauki, domin su samu sauki daga wahalhalu da tsadar rayuwa da suke fama da ita a halin yanzu.
Ya ci gaba da cewa duk, da gwamnatin ta gaji matsalar tsaro ne, amma ya kamata ta kara kokari wajen magance ta, kuma masarautar za ta ci gaba da taya gwamnatin da addu’o’i domin samun nasara.
Game da shirin dauke FAAN da sassan CBN daga Abuja zuwa Legas kuwa, sarkin ya ce lallai ya kamata Tinubu da ya sake tunani domin “kau da tunani mara kyau a cikin al’umma.
“Idan kuma abubuwa na alheri ne (a cikin shirin), sai a sanar da (jama’a) su, don su fahimta, domin a hada kai a samu ci gaba.“