✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakon ‘yan makaranta

A hir da halin kusu a wajen makarantaAssalamu alaikum daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido. Ina ma addu’a da fatan alheri darajar wannan wata…

A hir da halin kusu a wajen makaranta
Assalamu alaikum daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido. Ina ma addu’a da fatan alheri darajar wannan wata mai alfarma na kame  baki da masu aikata sauran laifuffuka, Mai -ya karbi ibadummu, kuma yasa mu ga na badin badada lafiya.  Ina kira ga k dalibai a ko’ina suke an sansu da ladabi da biyya da rashin kin zuwa makaranta  akan lokaci, da su rika maida hankali, tare da zage damtse wajen koyon watsatstsake da buda wagagan litattafai da mayar da hankali don gudun ba mara da kunya ga iyaye da ma abokan zama, wajen zana jarabawa, don gudun a  kada a samu dalibi da yin na kusu a dakin jarabawa.
Da a samu dalibai masu halin kusu a wajen zana jarabawa gara a maimaita, ya fi ko ‘yan makaranta?. Koma ta haka ake samun karkacewa ga shagabanni, musamman idan mun yi la akari da halin da muke ciki yanzu.  Daga: Abdullahi Kabir 07063147617 Baci-rawa Jihar Tumbin giwa.
Muna bukatar na-kwadi
Bayan sallama da salama a cikin wannan wata mai albarka da dukkan dalibai da ma masu duba wagegen wannan shafi mai alfarma na makarantar Dodorido. Sanin kowa ne a cikin wannan wata mai albarka watan rahama da al’umma suke bukatar na kwadi a kowanne lokaci wajen fandam-fandam ko jika makoshi. Sai ga shi mu a Jihar Zaman-fara ko Mu-muka fara shari’a, abin ba haka yake ba domin sai muyi kwana kofar hanci  ko ma ince kwana kwanciyar magirbi, bamu ga na kwadi ko dis-dis ba a kofar  famfoo ba. To kowa yasan yadda na kwadi yake da matukar amfani ga al’umma domin har ana kamfai da shi a wajen talakawa ga shi samunsa sai an kai ruwa  rana. Ina kira da wannan bangare ya maida hankali don kwararo mana na kwadi don musha, mu yi tatul.  Daga AbdulNasir lawal P.R.O (ROCKY) Jahar mu-muka-fara shari’a.
Adon-gari da iyayen giji a daina tabara
Bayan gaisuwa irin ta addinin gaskiya ga daukacin daliban wannan makaranta da Dodorido da ma sauran al’umma baki sili, ina muna fatan kowa ya tashi da uwar jiki lafiya. Ina kira da ‘yan uwana mata da su  zama masu dabi’ar damo a duk inda suke. Badon  ba, sai don su ne sikiyarin rayuwar dukkan wani mutum, kuma mata su ne fitilar dukkan wani mahaluki.
Ya ku ‘yan uwa na masu daura dankwali da  mu himmatu wajen dagewa  da asassa abin alheri don gaba. Bayan haka kuma ‘yan uwana adon gari da iyayen giji mu yi hattara wajen kame baki, don a daina sakin sa ratata kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya yi ta zuba, kamar indararo, ko a gida, ko a hanya ko a gidan biki. Abin babu ta-ido a ce adongari ko uwargida ta gari indai ba mai gararamba ba, wadda ta saba shiga gari da garin kwaki a jakar ta ba; wadda da ta samu guri ta jawo, ba tare da ta jika ba, ta kama sha, musamman ma a farfajiyar turke ababen hawa na haya. Wannan ba adon gari tagari bace, don ko  a gida ba za ka same ta da kamun kai ba. Idan munyi la’akari da wasu ‘yan uwa na mata a gidan biki, sai ka ga sun saki baki kamar ma ba su yi kuriciya ba, don a nan za ka ji ana shewa, kamar shawa ta kwance; kai an sassauta daurin zane, an cire dankwali, idan ma hijabi ne an cire, an jefar gefe guda; gashi na mujiya ya rufe, ba a ganin ko suwa ye a tsaye, ballantana ma masu kai ko mo, kaico wahayin zance ya sauka ga wannan  mata, ko irin wannan mata basa tunanin ‘yan dugwi-dugwi suna zagaye da su?.
Abu na gaba kuma shi ne, a duk lokacin da ka ga ‘yan uwa adon gari sunyi ayari, to kai ka ce gurin gada za su don zance ba kakkautawa, ana tafiya ana buga kafa, wani lokacin ma har da gyatuma.. Don Mai-duka Iyayen giji da adon gari a daina tabara, mu kula  da irin wannan aika-aika don wata rana ‘yan dugwi-dugwi din mu ne za su aikata irin wannan, Mai-duka ya shirya mu  duk wanda ya karanta  ya ce amin. Daga: Hafsat 07032138614 Jahar Tumbin Giwa    
A dubi gidan Bokan Turai da ke yashe
Assalamu alaikum daliban wannan makaranta tamu mai albarka ta Dodorido da ke cikin shafin Aminttar jaridar da ake bugawa a kasar Haurobiya, jinjina da reshenta na Jihar Tumbin giwa. Magana ta dokin karfe, ba zance irin ta ‘yan Damo-da-Kada-Diya ba, sai na je Jihar Bayan kada ba, zan tsaya ne akan titin gidajen namun daji da na mai sunan ‘ya’yan itaciyar na Jihar Birnin Dabo, wanda shekararren gwamnan ya bijiro da aikinsu kafin ya dire,. to munga ya tsaya tsak kamar tsinken tsire a kan tukuba. \
Sanin  ne a kasar Haurobiya Gwamnan kwan-kwatsatstsiya yana kwan-kwatsa wa jihar Tumbin -Giwa ayyukan alheri, don haka.muke kira gare shi da ya duba wadannan gidajen Bokan Turai nan na dis-ya kalleso da na mujiya don sanin kowa ne jiya ba yau ba, da a kammala mana gidajen bokan amalala, don gudun malalowarsu ba tare da wani sashi gidan bokan turai a jahar. Bayan haka don gudun kada al’umma su rika tsallakewa zuwa kasashen ketare, tunda mun san ka tura ‘yan dugwi-dugwi din talakawa zuwa kasashen ketare don koyon watstsaken Bokan Turai,don da sun kammala, su dawo su taimaka wa al’ummar mu, da ciyar da kasa ta gaba da ma Haurobiya baki sili. Daga: Aliyu  Bokan Turai, Jahar Tumbin Giwa 08147475769.
Batun Idi Mai kati
Assalamu alaikum daliban wannan makaranta tamu mai albarka ta Dodorido da ke cikin shafin Aminttar jaridar da ake bugawa a kasar Haurobiya. Jinjina ga ma’aikatanta, wadanda ba sa tata-tata kodayaushe, musamman Direban Alin wannan makaranta, malam DODO.  Shagaba na kasa yana shelanta wa dukkan shagabanni na rikon wannan makaranta na jihohi cewa idan mun koma gidan Tunau da aka fara zama a jihar Tumbin giwa, an bijiro da abubuwa da dama. To a yau ba sai gobe ba maganar IDI-MAI-KATI  ce ta taso ga dukkan ‘yan wannan makaranta ta Dodorido, domin duk inda suka shiga su rika bada colo; domin duk inda ‘yan makaranta suke  su kara kwazo. Kuma baya ga neman na dan kanzo,  indai ya dage da watsatstsake da buda wagawagan litattafai babu shakka za a rika bashi choko-milo  a aji e she.
Domin yadda abin zai kasance duk wani shagaba na jiha zai ba mu cikakken  matsugunni direshinsa , ta yadda  idan shagabanni na kasa sun kammala bayanai za su ba su sakon ya same su dirshan, don su sanar da daliban su kan tsarin IDI-MAI-KATI. Mahimmancin IDI-MAI-KATI ba sai na fadda ba,  kowa ya sani in dai yana zagayawa a kasar Haurobiya da ma ketare. Kai in ta kai ta wani gurin ma ba ka isa ka kketara ba, har idan baka da shi, sai mun gani daga .Daga:Aliyu Mukhtar Sa’du Jami’in hulda da Jama’a na kasa 08034332200.
Gangamimn Dodanni a bayan Idi
Bayan sallama  irin ta masu kadaita Mahallaicci sili, muna sanar da ‘yan makarantarmu mai albarka ta Dodorido na jihar Tumbin-Giwa in Mai-duka ya kaimu.bayan Idi, da anyi sallama ta salla hada salamtu da sallau sai su sulale sarab na sadab su yi wo cincindo ko ba cin-cin, domin ba ma yaren chong-chong, sai namu  na dor-dor da ake a kasar Haurobiya. Akwai shagabannin wannan tsari kamar haka.
1. Halliru Kabir Gogel Shagaba 08039336748
2. danladi Mai neman na aure (DANBATTA) 08063043322/08070882813
3. Saifullahi Idris Bilyaminu (S.I.B) 08031122523
4. Bashir Muhammad Dandago 07038652537.
Daga:Jama’in hulda jama’a na Jihar Tumbin-Giwa. Umar Muhammad Abdullahi 08067676454.
Zabi-sonka mai karatowa: Hattara masu jini a jika
Assalamu alaikum daliban wannan makaranta tamu mai albarka ta Dodorido da ke cikin shafin aAminttar jaridar da ake farfasata, da shinmfida ta a kasar Haurobiya. Idan Mai-duka ya kaimu  a shekara ta dubu karamin lauje da zagaye da sili da babban lauje za a yi zabbi sonka a matakin kasa. Sanin kowa ne idan irin haka ta taso masu irin wannan tasu bukata sukan bijiro da bukatu iri-iri ga zuki-ta-malle a wajen kamfato ayyuka, har da ma kanzon kuregen batutuwa barkatai, musamman ma na bantso tun da ba tsaro a kasar ga kamfen na samar da gora ko’ina, amma a gidajen talakawa ko oho, sai dai a gidajensu da inda suke kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma.  
Idan mun je gidan Tunau, jama’a ku ne shaida duk lokacin irin wannan idan ya taso akan sa iyayen giji da masu jini a jika don su je su yi ta kada kuri’a, su kuma shagabanni suna ta keta musu dariya hahaha! Bayan sun ba su koko na rana daya, ko sabulu ko damin Hauro kalilan wanda daga karshe ba zai tsinana masu komai ba.
Hattara jama’a da a hankalta kada a yi zaben tumun dare a shekara ta dubu karamin lauje da zagaye da sili da babban lauje. Jama’a a daure a zabi ingantattun jagorori. Daga: Hafsatu Jihar Tumbin Giwa 07032138614.
Martanin Barau dan canji
Batu na waskiya ma su neman na dunduma kururu a rumfar Barau dan canji su na cikin gararin a karkashin  mulkin jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, musamman Arewatawan Haurobiyawa. Ga matsalolin rashin tsaro sai tsagwaron tsoro, ga kuma wayon a ci wai an kori durwa daga dinya.
Allah sarki! Talaka bawan Mai- duka. Ina ma yaran rumfar Barau za su dauki shawarwarin Babban Direban Alli? Lallai da sun mori romo na neman abin dundume kururu cikin fasahar yanar gizo a asusu babu ruwan su da sususu ko kusu.
Don kada su yi zuru a maishe da kowannen su sususu, su yi  batan baki, su yi belbel ba su ga mai shawagi da fuffukai, ba su ga tarin koko. Ni ma dai hankali na ya fi ga na duke. Mu yi koyi da mutanen Bankin-koko, ba kuma bukatar hawa shoridon bisa don ziyarar TayaLandan. Domin kuwa tun kafin a haifi Innar mai sabulu balbela take shafe da hasken farar kasa. Ehe!
Daga Ashiru dan Azumi Gwarzo. [email protected] +2340703 658 9807
Ban fahimci Dodorido ba
Assalamu alaikum tare da fatan kana lafiya. Na rubuto wannan sakon ne, domin tambaya a gareka Don Allah wannan shafin naku *DODORIDO* mece ce ma’anarsa? Sau da yawa nakan karanta shi a cikin jaridar Aminya, amma na kasa fahimtar komai a kai. Daga [email protected]