Gwamnatin jihar Gujarat da ke Indiya ta saki wasu mutum 11 daga kurkuku wadanda kotu ta daure bayan samun su da laifin yi wa wata musulma fyade, duk da kotu ta yanke musu hukuncin daurin rai da rai.
An saki mutanen ne a ranar Litinin bayan sun yi zaman gidan yari na shekara 14 daga cikin hukuncin da kotu ta yanke musu na rai-da rai.
- Sun shekara 8 suna gudanar da ofishin ’yan sanda na bogi a otel din Indiya
- An kama matsafa da busassun gawarwaki 20 a Edo
Mutanen mabiya addinin Hindu sun yi wa matar mai suna Bilkis Bano fyade ne, kuma suka kashe ‘yarta mai shekara 3 da haihuwa a yayin wani rikicin addini a wani kauye da ke kusa da birnin Ahmedabad.
A ranar uku ga watan Maris na shekarar 2002 lokacin da abin ya faru, Bilkis tana ‘yar shekara 19, kuma tana dauke da juna-biyu.
Bayan ita, mutane sun yi wa mahaifiyarta fyade, sannan suka kashe ‘yarta mai shekara uku da haihuwa.
A jimlace dai sun yi wa iyalinta da danginta 14 kaca-kaca, ita kadai ta tsira da rai da kuma wasu ‘yan uwanta biyu.
Da aka kama masu laifin, sai da aka kai ruwa rana tare da matsin lamba, sannan kotun ta tabbatar da laifinsu kuma ta yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai a shekarar 2008.
Gwamnatin yankin Gujurat ce ta jam’iyyar ‘yan gani-kashenin Hindu ta BJP ce ta yanke shawarar sakin mutanen wanda ya tayar da hankalin ‘yan kasar, ya kuma janyo kace-na-ce.
A karkashin dokar Indiya dai, bayan shekara 14 za a iya sakin wasu firsunonin da suka nuna nadama, idan kuma sun cika wasu ka’idoji na gyaran hali da yawan shekarun haihuwa, da kuma girman laifi.
Amma a cewar ‘yan adawa, wannan son kai ne da bangaranci da kuma rashin adalci.