✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bollywood: Kalubalen da fina-finan Indiya ke fuskanta

Ba mu taba ganin wannan musifar ba.

Fina-finan Indiya na fuskantar rashin kasuwa a manya-manyan sinumu da gidajen kallo na kasar wadanda a da, mutane ke turuwar zuwa kallo.

Finafinan Indiya a wurin Hausawa, wadanda su ka samu suna daga ‘Hindi’ a kasar ta Indiya, sannu a hankali suna durkushewa ta fuskar daukaka.

Gidajen Sinimomi sun yi tsit, kudin shiga daga wannan bangare ya yi kasa, tun lokacin da aka sakar wa mutane mara daga takunkumin annobar COVID-19.

“Ba mu taba ganin wannan musifar ba”  in ji wani mai gidan sinima Manoj Desai a hirar sa da AFP.

“A cikin finafinai 50 na Bollywood da aka saki a shekarar [2021] da ta wuce, ‘yan kadan ne su ka yi rawar gani saboda annobar Coronavirus.

“Wasu kalilan kuma suka mayar da kudinsu, ko kuma suka samu ‘yar riba,” in ji Karan Taurani, wani mai nazari kan al’amuran yau da kullum na kasar.

Bollywood kamar sauran masana’antun shirya finafinai na sauran kasashen na fuskantar kalubale daga hanyoyin kallon finafinai na zamani da suka soma shigowa kafin annobar COVID -19.

Yanzu kuma suka yi tasiri tare da dauke miliyoyin Indiyawa masu kallo a lokacin da a ka sanya dokar zama a gida.

Kasar mai yawan mutane biliyan 1.4, sama da rabin su, na iya shiga Intanet su kuma kalli tasoshin Netflix da Amazon Prime da kuma Disney+.

A cewar wani rahoton gwamnatin kasar kuwa, tashar Hotstar ita kadai tana da masu kallo miliyan 96.