Babban kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa, Zariya ta dage ci gaba da sauraron karar da ake yi wa mutumin nan da ake zargi da yin garkuwa da ’yar cikinsa.
An dai gurfanar da mutumin ne bisa tuhumarsa da laifin kai ‘yarsa zuwa wajen masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
- ‘Yan bindiga sun sace mara lafiya da ke kan gadon jinya a Zariya
- Yadda muka kama ‘masu daukar nauyin ta’addanci’ a cikin banki a Zariya – Sojoji
Da yake amsa tambayoyi daga Lauyar wadda ake tuhumar, wanda ya kai kudin ga masu garkuwan da suka bukata, kuma da ga wacce aka yi garkuwan da ita, ya kara tabbatar da cewa shi ne ya kai kudin da aka bukaci su biya na fansar mahaifiyarsa.
Aminiya na bin yadda shari’ar ke gudana ne sakamakon sakin da kotun farko ta yi wa mutumin a kan mika ‘yar uwarsa ga masu garkuwa da mutane a dajin Galadimawa, inda ta kwashe tsawon kwana 60 a hannunsu.
Daga bisani ita ma Babbar Kotun ta sake ba da belinsa domin ya je ya nemi magani a dalilin rashin lafiya da aka ce yana fama da ita.
Sai dai masu bibiyar yadda shari’ar ke gudana sun ce, shari’ar ta na tafiyar hawainiya, kuma ana ta wahalar da shaidun da ita kanta wacce aka yi garkuwan da ita, yayin da wanda ake tuhumar yake ta more belin da kotu ta ba shi