Kungiyar kare hakkin dan Adam ta ‘Amnesty International’ ta ce take hakkin bil Adama da rashin martaba doka ne dukan Musulmi da ’yan sandan kasar Indiya suka yi.
Kungiyar ta yi wannan furuci ne bayan bidiyon da ya karade kafafe sadarwa na zamani a kwanan nan wanda ke nuna yadda jami’ai suka yi ta runtuma wa wasu Musulmi sanda.
- Yadda Tafiyar awa 2 ta dauke su wata 7 a Jirgi
- Tsohon dan sanda ya kashe mutum 34 da iyalansa a Thailand
- NAJERIYA A YAU: Shin kayyade Kudaden Kamfen Zai Kawo Zabe Mai Tsafta a 2023?
A bidiyon lamarin da ya auku a kauyen Udhela da ke gundumar Gujarat Kheda, an ga yadda aka turke wadanda lamarin ya shafa da wuta aka yi ta labta musu sanda a mazaunansu.
Sai dai kuma wasu bayanai daga yankin sun ce, ’yan sandan sun dauki wannan mataki a kan matasan ne kan zargin jifan su da duwatsu a wajen wani taron mabiya addinin Hindu.
An ce bayan dukan da suka sha a hannun ’yan sandan, an kuma bukaci wadanda matasan da su bai wa taron hakuri kafin daga bisani aka ingiza su cikin motar ’yan sanda aka tafi da su.