Kotun Kolin kasar Indiya ta halasta wa mata marasa aure a kasar zubar da ciki a duk lokacin da suke so.
Kotun ta ce marasa aure daga matan Indiya suna da damar zubar da cikin da ya kai mako daya zuwa makonni 24, hukuncin da masu rajin kare hakkin mata a kasar suka yaba da shi.
- Za mu sanya wa jam’iyyu ido kan kudaden yakin neman zabe — INEC
- Mahaukaciyar guguwar ‘Ian’ ta raba Amurkawa 2.5m da muhallansu
Batun halasta zubar da ciki na ci gaba da samun karbuwa a sassan duniya tun bayan da Kotun Kolin Amurka ta halasta hakan a kasarta.
A ranar Alhamis, alkalin Kotun Indiyar, Mai Shari’a D.Y Chandrachud ya yanke hukuncin cewar rashin aure ba zai hana ’yan mata zubar da ciki ba duk lokacin da suka bukaci hakan.
Tun a 1971 dokar zubar da ciki a kasar ta takaita aikata shi ga matan aure da zawarawa da mata masu lalurar tabin hankali da sauransu.
Amma sai a wannan karon ne ’yan mata marasa aure suka samu shiga jerin wadanda aka halasta wa zubar da cikin a kasar.