✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saki ko duka?

Wani maigida ne suka samu sabani da matarsa, a maimakon ya yi mata nasiha, kawai sai ya fara dukanta. Yana cikin dukan nata can sai…

Wani maigida ne suka samu sabani da matarsa, a maimakon ya yi mata nasiha, kawai sai ya fara dukanta. Yana cikin dukan nata can sai ga abokinsa ya zo, ya ga abin da ke faruwa. A nan ya dakatar da maigidan daga dukan da yake yi wa matar, ya kuma tambaye shi abin da ya faru. A nan ne maigidan ya kwashe labari ya fada masa, sai abokin ya ce: “To kai in ban da kai wa yake dukan mata? Tun dai bata maka rai take yi, sai ka auro mata abokiyar zama.” Matar tana jin abin da abokin nan ya fada, nan take sai ta ce: “Maigida don Allah manta da shi, ci gaba da duka na.”
Daga Isah Ramin Hudu Hadeja, 08060353382