✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

Rundunar Sojin Ƙasan Najeriya ta sallami wata ƙurtu sojan da ta zargi wani babban soja da yunƙurin yin lalata da ita

Rundunar Sojin Ƙasan Najeriya ta sallami wata ƙurtu sojan da ta zargi wani babban soja da yunƙurin yin lalata da ita.

Rundunar ta ce ta sallami ƙaramar dokar mai muƙamin Private daga aiki ne bayan ta kammala bincike kan zargin da ta yi.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa bayan kammala zuzzurfan binciken da aka gudanar, an gano cewa babu ƙamshin gaskiya a zargin da Private Ruth Ogunyele ta yi wa Kanar I.B Abdulkareem.

Amma ya ce duk da sallamar ta daga aiki da aka yi, za a biya ta kudaden garatuti kuma za ta rika karɓar fansho.