✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno

Akalla mutane hudu sakamakon kifewar wani kwalekwale a Karamar Hukumar Dikwa da ke Jihar Borno

An tabbar da rasuwar akalla mutane hudu sakamakon kifewar wani kwalekwale a Karamar Hukumar Dikwa da ke Jihar Borno.

Kakakin ’yan sanda a jihar, ASP Kenneth Daso, ya sanar a ranar Talata, cewa “hatsarin kwale-kwale ya afku a ranar 23 ga watan Satumba, 2024 a yankin Bakassi da ke tsakanin Mafa da Dikwa a kan hanyar Maiduguri, inda ya yi sanadin asarar rayukan mata hudu.

“Wadanda suka mutu, dukkansu ’yan unguwar Bulabulin, Dikwa, kuma an gano su, an kai su babban asibitin Dikwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

“Daga bisani an mika gawarwakin ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”

Kwamishinan ’yan sandan jihar, ML Yusufu, a yayin jajantawa, ya bukaci mazauna yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, da su yi taka-tsan-tsan a wannan lokaci, tare da gaggauta kai rahoton duk wani lamari na gaggawa.