✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakatare ya bukaci a rika tallafa wa marayu

Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Filato Alhaji Salisu Musa ya bukaci al’ummar Musulmi ta tashi tsaye wajen tallafa wa marayu don saukaka musu kuncin rayuwa…

Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Filato Alhaji Salisu Musa ya bukaci al’ummar Musulmi ta tashi tsaye wajen tallafa wa marayu don saukaka musu kuncin rayuwa da suke fuskanta.
Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen mika kayan tallafi da Kwamitin Mata masu Tallafa wa Marayu na Unguwar Gangare a garin Jos Jihar Filato, karkashin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ya mika ga marayu 100 ga makon jiya.
Ya ce akwai lada mai yawa a cikin tallafa wa marayu don haka ya kamata al’ummar Musulmi su tashi su tallafa wa marayu. Sai ya yi kira ga Musulmi su ji tsoron
Allah, don samun mafita kan mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya.
Shugaban matasan kungiyar Izala reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa Malam
Kabiru Muhammad Cidawa ya yaba wa shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau kan kirkiro wannan shiri na tallafa wa marayu.
Ya ce ganin yadda shirin ya kankanma a karamar hukumar ya sanya suka kafa kwamitin mata a unguwar.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi su tashi su tallafa wa marayu bisa lura da dubban marayun da ake da su a kasar nan sakamakon rikice-rikicen da ake fuskanta.
Tun farko a jawabin shugabar kwamitin Malama Rahina Yusuf Yakubu ta ce sun kafa kwamiti ne don su taimaka wa marayu ganin yadda jama’a ta tsinci kanta a mawuyacin hali na rikice-rikicen da aka yi fama da su a jihar a baya.
Ta ce a wannan taro sun tallafa wa marayu maza da mata100 da atamfofi da yadikan shaddoji da takalma kuma sun biya wa wasu kudin jinya a asibitoci.
Ta yi kira ga sauran al’umma su kafa irin wadannan kwamitoci domin rage matsalolin da marayu suke ciki a kasar nan.