✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sa’in Katagum ya rasu yana da shekara 85

Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Danmadami Sa’in Katagum rasuwa. Marigayin ya rasu yana da shekara 85  kuma yana daya daga cikin dattawan Arewa. Sa’in…

Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Danmadami Sa’in Katagum rasuwa. Marigayin ya rasu yana da shekara 85  kuma yana daya daga cikin dattawan Arewa.

Sa’in Katagum wanda tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda Najeriya ne,  ya rasu ya bar babban wansa Kilishin Katagum Alhaji Dansidi da mata uku da ’ya’ya 27, ciki har da Alhaji Nura Danmadami, Darakta a Ofishin Kula da Basussuka da kuma wani Babban Jami’in Kwastam Alhaji Ahmed Danmadami da sauransu.

Mamacin ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya kuma Babban Limamin Katagum Malam Ayuba ne ya jagoranci Sallar Jana’izarsa, inda bayan Sallar ya bayyana marigayi Danmadami a matsayin mutumin kirki mai tsoron Allah, mai halaye nagari abin koyi wanda al’umma suka amfana da rayuwarsa, sannan ya roki Allah Ya jikansa Ya gafarta masa kura-kuransa.

Cikin wadanda suka halarci jana’izarsa akwai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Mahmud Yayale Ahmed, da Wakilin Sufeto Janar na ’Yan sanda Mataimakin Sufeto Janar da ke kula da shiyya ta 12 ya wakilce shi, da ’yan Majalisar Sarkin Katagum, da al’ummar Masarautar Katagum da dama.

Daya daga cikin ’yan uwan marigayin, Alhaji Baba Sa’idu Sa’in Toro ya ce bayan marigayi Danmadami ya yi ritaya daga aikin dan sanda a ranar 31 ga watan Disamba a 1983, sai ya koma ayyukan addini da kuma kula da ayyukan kyautata rayuwar al’ummarsa.

Ya ce marigayin mutum ne wanda ba ya wasa da ayyukan addini domin mutum ne mai yawan ibada da zikiri da Sallah da karatun Alkur’ani da salatin Annabi, kuma a kullum kokarinsa ya bi koyarwar addinin Musulunci. Ya nuna cewa za a dade ana tuna shi saboda nagartattun halayensa da kuma dabi’unsa da yadda yake taimako da tarbiyyantar da al’umma.

Alhaji Sa’idu ya ce bayan marigayi Sa’i ya bar aikin dan sanda, ya taba zama Babban Daraktan Bankin First Bank, mukamin da ya rike na tsawon shekara bakwai daga 1984, sannan daga baya ya ajiye aikin. Ya kuma taba rike mukamin Babban Daraktan Bankin Inland Bank wanda yanzu ya koma Bankin FCMB, sannan ya taba zama Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Bauchi, ya kuma zama jagora kuma Shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi lokacin Gwamna Ahmadu Muazu.

Shi ne kuma shugaban fafutukar neman kirkiro sabuwar Jihar Katagum daga Jihar Bauchi, sannan ya samu horo a NIPPS da ke Kuru cikin Jihar Filato.