Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya rattaba hannu kan dokar tilasta wa ’yan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa biyan Naira miliyan 10 kafin kowannensu a ba su izinin nuna fosta da allunan talla a jihar.
Dokar ta wajabta wa ’yan takarar gwamna biyan Naira miliyan biyar, masu takarar Sanata kuma Naira miliyan biyu, ’yan takarar Majalisar Wakilai Naira miliyan daya, sai ’yan takarar Majalisar Dokokin jiha Naira 500,000.
- NBC ta haramta sanya wakar Ado Gwanja a rediyo da talabijin
- Malamin da ya ki karbar aiki a Dubai don kishin Najeriya ya koka kan yajin aikin ASUU
Sabuwar dokar tallace-tallace ta shekara ta 2022 na daga cikin wasu kudirori uku da gwamnan ya rabbata hannu a kai domin su zama doka a jihar.
Gwamna Bello ya ce sababbin dokokin da aka sanya wa hannu za su taimakawa wajen tabbatar da tsaftar muhalli da karuwar kudaden shiga.
Yahaya Bello ya bukaci ’yan majalisar dokokin jihar da su zakulo duk wasu dokokin da aka sanya wa hannu a baya, amma ba a aiwatar da su a ma’aikatu ko hukumomin jihar domin a hada gwiwa da sa ido wajen aiwatar da su da tantancewa.
Gwamnan ya kuma bukaci majalisar ta ci gaba da yin aiki tare da sauran bangarorin gwamnati domin yi wa al’umma hidima.
Sauran dokoki da aka rattabawa hannu sune Dokar sokewa da sake fasalin otal da Hukumar Yawon shakatawa na 1995; da dokar Kafa Hukumar Kula da yawon bude ido ta Jihar Kogi da sauran batutuwan da suka shafi hakan.