Malama Bilkisu Yusuf Ali marubuciya kuma hazikar sha’ira ce. Ta rubuta littattafai da dama, wadanda suka kara tabbatar da ita cikakkar marubuciyar da ake alfahari da ita a duniyar marubuta Hausa. A wannan tattaunawa da ta yi da Aminiya, marubuciyar ta bayyana al’amura daban-daban da suka shafi rayuwarta da kuma ta harkar rubuce-rubuce:
Ko za ki bayyana mana tarihinki a takaice?
Sunana Bilkisu Yusuf Ali. An haife ni a Kano a shekarar 1977. Na yi karatun firamare a Gandun Albasa Special Primary School, bayan na gama sai na tafi makarantar sakandare ta Women Arabic Teachers’ College da ke Goron Dutse. Na yi digirina na farko da na biyu a Jami’ar Bayero Kano.
Yaushe ne kika fara rubuce-rubuce kuma me ya ja hankalinki har kika ga cewa ya kamata ki fara rubutun?
Na fara rubutu a shekarar 2000. Dalilin da ya sa na fara rubutu, na farko dai sha’awa ce; domin tun ina karama ina da son karance-karance har kuma na girma ban daina karance-karancen littattafai ba da jarida da mujalla har yau. Baya ga sha’awa, ni na tashi gidan malanta tun da na budi ido wa’azi na gani mahaifina, Shaikh (Dokta) Yusuf Ali yake yi. Baya ga aikinsa na gwamnati ba ya da wani abu fiye da wa’azi da shiryarwa, don haka na yi tunanin ni ma na taimaka wa al’umma ta hanyar fadakarwa da nishadantarwa da wa’azin lokaci guda. Bayan na fada masa kudirina ya amince tare da sa albarka. A haka littafina na farko ya shiga kasuwa cikin fargaba amma karbuwar da littafin ya yi sai ya ba ni karfin gwiwa na ci gaba da rubuce- rubucena har zuwa yau.
Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta kuma guda nawa ne aka buga suka shiga kasuwa?
Ina da littattafai guda goma zuwa yanzu, wadanda suka shiga kasuwa. Ga su nan kamar haka: 1-Sai Wani Ya Zubar. 2-Inuwar Bagaruwa. 3-Wutar Kara. 4-Sa’insa. 5-Tarnaki. 6-Maye Gurbi. 7-Uwar ’Ya’ya. 8-Halin-Ni- ’Yasu. 9-Takun Saka da kuma na 10-Bakin Bunu.
A wane yanayi kika fi jin dadin yin rubutu?
Na fi son rubutu cikin dare ko lokacin da nake ni kadai.
Ko kin taba samun kyauta ko karramawa ta dalilin rubuce-rubuce?
E, na samu Kambun Girmamawa, wanda Hukumar Tace Fina-Finai Da dab’i da hadin gwiwar kungiyar Marubuta Ta kasa (ANA) ta ba ni a bana. Sannan na samu shaidar yabawa daga kungiyoyi da dama. Daga cikinsu akwai kungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero Kano da kungiyar Tsangayar Adabin Hausa da kungiyar ANA Reshen Jihar Kano da kungiyar Marubuta Hausa (HAF).
Ko kin gamsu da yadda harkar rubuce-rubuce take a duniyar Hausawa?
Gaskia rubutu a nahiyarmu ta Hausa akwai matsaloli a dukkan bangarorin uku, wato marubuta da makaranta da kuma al’umma da su ba su karatun amma suna gefe suna yanke hukunci. Bari mu fara da marubuta, wadanda suke bukatar hadin kai da bita a kai-a kai na musamman don inganta rubutu da bincike kafin rubutu da takaita fitar littattafai barkatai.
Alhamdu lillahi, yanzu kam an samu ci gaba kwarai don marubuta sun yi wa alkaluminsu linzami, babu korafe- korafe a yanzu, babua rubutun batsa ko soki burutsu amma duk da haka an ce in kana da kyau ka kara da wanka. Marubuta suna bukatar bincike na kwarai kafin gabatar da kowanne rubutu.
Makaranta su ma suna kawo nakasu a harkar rubutu. Ba su ba marubuta dama ta rubuta ra’ayinsu yayin da marubuci ya yi rubutu ya saba ra’ayinsu sai ka ji sun aibata littafin ko ma su bi duk yadda za su yi su kashe kasuwar littafi ko ma su dusashe marubuciyar. Ba su la’akari da dai ko hangen marubucin shi ne daidai ko kuma kuskure ne na marubucin wanda shi ma mutum ne kamar kowa, yana iya yin kuskure. Zabe da makaranta ke yi shi ma yana janyo nakasu kwarai, musannanma ga sababbin marubuta.
A bangaren al’umma kuwa, na farko muna fuskantar rashin karatu. Mutanenmu ba su son karance- karance. Ko wadannan littattafan namu masu karanta su kebabbun mutane ne, wato mata da matasa. Wannan kuskure ne, domin kuwa al’umma sun dora littattafan a kuskuren fahimta. A hangensu ba komai ciki sai sharholiya, wanda ba haka ba ne. Littattafan nan cike suke da ilmantarwa da fadakarwa a kan duk nau’o’in rayuwa, musamnan zamantakewa da mu’amala da addini da al’ada.
Ko kina cikin wata kungiyar marubuta? Wace irin gudunmowa irin wadannan kungiyoyi suke bayarwa ga harkar rubuce-rubuce?
E, ina cikin kungiyoyin marubuta da dama. Ina cikin kungiyar ANA Reshen Jihar Kano, inda ni mamba ce. A kungiyar Mace Mutum, ni ce Jami’ar Walwala. A kungiyar HAF, ni mamba ce. A Tsangayar Adabin Hausa, ni ce Ma’aji. A kungiyar Kallabi Writers’ Association, ni ce Sakatariya. Haka ma a kungiyar Hausa Writers’ Association of Nigeria, ni ce Ma’aji.
kungiyoyi na taimakawa kwarai wajen ci gaban marubuta da hadin kai da taimakekeniya da tafiya da murya guda a wasu lokutan. Sai dai batu na gaskiya, har yanzu kungiyoyin marubuta ba su taka rawar da ya dace dari bisa dari. Wannan na faruwa ne ko dai don rashin karfin kungiyar ko hadin kan ’ya’yan kungiyar, wanda da marubuta za su ba kungiya dama da goyon baya dari bisa dari da sun mori romon kungiya. Haka su ma a shugabannin kungiyar, su sa Allah a ransu; su sani cewa komai kankantar hakki abin tambaya ne, Allah ba Ya barin zalunci. Don haka ya kamata su kyautata niyya, su yi aiki tukuru fi sabilillahi don ciyar da adabi da ma rubutu gaba. Ya kamata kungiya ta zama tana share hawayen ’ya’yanta da nema musu hanyoyin ci gaba.
A matsayinki na marubuciya, mene burinki a nan gaba?
Burina a rubutu ya cika gaskiya, sai dai ka san dan Adam da hange-hange. Fatana ya zama fadakarwar da nake sakon ya shiga zukatan al’umma kuma alhamdu lillahi sako yana shiga cikin hikima da kaifin tunani. Ba wanda ya taba sukar rubutuna don na kauce wa al’ada ko addini, daidai gwargwado alkalamina a tsarkake yake. Ba na kunyar yarana ko wani ko nan gaba surukaina su daga su ga abin da na rubuta. Ko bayan raina ba ni da kaico in an ga me na bari don duk littafin da na rubuta mahaifina Shaikh (Dokta) Yusuf Ali shi ne yake fara karantawa kafin ma na saki littafin a kasuwa. Sai dai fatan Allah Ya kara shige mana gaba. Mahaifina Allah Ya yi masa sakayya da mafificin alheri, Ya ja kwanansa; domin da gudunmowarsa ne na kai duk inda na taka a yau.
Haka kuma akwai malamaina wadanda nake alfahari da su a duniyar rubutu, wadanda kullum suke kara ba ni kwarin gwiwa, suke nuna mini duk irin rubuce-rubucen da zan yi, na yi kar na ji shayi ko fargaba. Cikinsu akwai Farfesa Isa Mukhtar da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Sheikh Aminuddin Abubakar da Sheikh Muhammad Turi. Gaskiya ina alfahari da wadannan mutane a rayuwata ta duniyar Adabi
Ko kina da wani kira ko shawara ga ’yan uwanki marubuta da gwamnati da kuma al’umma dangane da harkar rubutu da wallafa?
Shawarata kullum ga marubuta ita ce, su dage su nemi ilimi kuma su nuna shi a rubuce-rubucensu. Sannan bincike na da matukar muhimmanci, kar su zama masu ci da zuci gun fitar da littafi barkatai. Su sani cewa da haihuwar yuyuyu gwamma da daya kwakkwara.
Al’umma kuma su daure su rika karanta littattafanmu, su daina yi mana kallon batattu. Su sani cewa mu wakilansu ne a al’ada da addini. Su rika sa ido, inda suka ga daidai su yaba, inda suka ga kuskure su gyara. Su sani cewa mu fa mutane ne kamar kowa, muna yin kuskure.
Ita kuwa gwamnati, kiran da zan yi mata ya ma fi na kowa, don mu ’ya’yan bora ne wurinta kan abokan sana’armu, wato ’yan fim. Mu ba ta ma san ma da mu ba, misali na kusa, ko a kwanan nan ta zage ta yi wa ’yan fim wadanda tare muke, mu ne ma kashin bayansu amma ta karrama su cikin girmamawa, sabaninmu. Duk harkokinta tana sa su gaba amma mu ta mayar da mu saniyar ware, wanda ba daidai ba ne. Mu ma muna da rawar takawa, inda ake zabar su a ba su mukamai a gwammati; mu ma a ba mu.