Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce ya kusa zubar da hawaye bayan ganin irin ta’adin da aka yi wa jihar Legas sakamakon zanga-zangar #EndSARS.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa takwaransa na jihar Babajide Sanwo-Olu ziyara a ranar Alhamis.
- Za a yi wa ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS karin girma
- Yadda aka yi arangama tsakanin kungiyoyin asiri a Legas
- #EndSARS: Ministoci da gwamnonin Kudu sun ziyarci Legas
- ‘A kamo barayin kayan tallafin COVID-19 na Kaduna’
El-Rufa’i ya ce Sanwo-Olu ya yi duk iya kokarinsa wajen ganin ba a samu tashin hankali a jihar ba, amma bata-gari sai da suka yi amfani da zanga-zangar wajen lalata kayan al’ummar jihar.
Ya ce “Na dauki tsawon lokaci ina duba hotunan yadda aka yi wa Legas barna, sai dana kusa zubar da hawaye ganin yadda aka lalata dukiyoyin al’ummar da su ke samar da ayyukan yi ga matasa.
“Bayyana bacin rai ga irin zaluncin ‘yan sanda ba laifi ba ne, amma lalata dukiyar al’umma ba komai bane face kawo nakasu da koma baya” inji shi.
El-Rufa’i ya nuna alhininsa ga iyalan ‘yan sanda da jama’ar gari da suka rasa rayukan ‘yan uwansu a sanadin rikicin zanga-zangar, tare da kira ga gwamantin tarayya ta kare faruwar hakan a gaba.
Shi kuwa a nasa bangaren, gwamna Sanwo-Olu, ya godewa El-Rufa’i bisa ziyarar jajantawar da ya kawo masa tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kawo karshen ayyukan wanda basa kishin ci gaban jihar.