’Yan kasuwa a wasu yankunan Najeriya sun bayyana cewa ba za su koma karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 ba, har sai sun ji Shugaban Kasa Muhamamdu da bakinsa ya ce.
’Yan kasuwa da kwastomominsu jihohin Kaduna da Legas da kananan hukumomin Abaji da Kwali a Yakin Babban Birnin Tarayya na kin karbar tsoffin kudin ne, bayan bankunan kasuwanci suka fara bayar da su, bisa umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN).
- Alakar sauya Kwamishinan ’yan sanda sau 5 a Kano da zabe
- NAJERIYA A YAU: Akwai Yiwuwar Sayen Kuri’a A Zaben Gwamnoni —Masana
Sai dai a Jihar Kano, harkokin kasuwanci sun fara komawa yadda aka saba, tun bayan da bankuna suka fara bayar da tsoffin kudi, kuma mutane suka ci gaba da amfani da su a harkokin kasuwanci.
Harkoki sun fara kankama a Kano
Wani tan kasuwa a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, Adamu Hamza, ya ce sun fara samun karuwar ciniki, “tsakanin jiya (Talata) da yau (Laraba), kudi ya fara yawo a hannun jama’a, suna kawowa kuma muna karba.”
Aminiya ta ruwaito cewa tun ranar Talata injinan ATM a birnin Kano suka fara bayar da tsoffin kudin, sai dai yawanci N500 ne.
Haka kuma an samu raguwa mutane da ke neman cirar kudi, dai dai wasu bankunan sun bayyana cewa tsabar kudin da ke hannunsu ya kare, shi ya sa ba a ganin layin mutane a ATM dinsu domin cirar kudi.
‘Sai mun ji daga bakin Buhari’
Aminiya ta zaiyarci yankin Abaji a ranar Laraba, inda ta iske mutane na ta gunaguni cewa bankuna sun koma ba wa mutane tsoffin takardun kudin.
Wani dan kasuwa, Bashir Aliyu, ya yi mana korafin cewa ya ce cikin banki cirar kudi , amma aka ba shi tsoffin takardun N1,000 da aka sauya, amma ya ki karba, sabo ba zai iya kashe su cikin sauki ba, idan ya je kasuwannin kauye.
Ya bayyana wa wakilinmu cewa, “Kasuwa Girinya nake zuwa sayen kifi da sauyan kayan abinci, kuma ’yan kasuwar ba sa karbar taransfa ko tsoffin kudi, shi ya sa da aka ba ni su a cikin na ki karba.”
A cewarsa, duk da cewa CBN ya ba umarnin bankuna su ci gaba da harkokinsu da tsoffin kudin, shi ba zai samu natsuwa ba sai sai ya ji Shugaba Buhari da kansa ya yi wa ’yan kasa magana cewa su ci gaba da amfani da tsoffin kudin.
Wani jami’in banki da ya nemi mu boye sunansa ya shaida mana cewa bankin ya fito da Naira dubu 500 na tsoffin takardun kudi da yake da su domin ba wa mutanen da suka zo cirar kudi, amma yawancin mutanen sun ki karba.
“A takaice, daga cikin N500,000 da bankin ya fitar domin ba wa kwastomomi N150,000 kadai aka samu wadanda karba,” in ji jami’in bankin.
Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu bankin nasu ba shi da sabbin takardun kudi, amma suna sa ran nan gaba CBN zai ba su.
Hakazalika wasu ’yan kasuwa a yankin Kwali na kin karbar tsoffin kudin, saboda har yanzu ba su ji Shugaba Buhari ya yi magana a kai ba.
Wata ’yar kasuwa mai suna Misis Laraba Gwatana ta ce, “Ni ba zan karbi tsohon kudi ba, saboda har yanzu rade-radi muke ji cewa CBN ya umarci bankuna su koma bayar da tsoffin kudaden.
’Yan kasuwa kaduna ma haka
Wakilinmu ya lura cewa maimakon karbar tsoffin kudaden, ’yan kasuwa da dama sun tanadi na’uarar tura kudi ta PoS ga kwastomominsu.
Wani dan kasuwa mai sayar da kayan gwari, Malam Lawal Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa, “ban fara karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 tukuna; amma ina karbar tsohuwar N200.”
Ya ce dalilinsa shi ne, “Gwamnati na ta kumbiya-kumbiya, don haka ina tsoron in karba, daga baya CBN ya ce ya canza shawara a bar ne da asarar biyan kudin kaya, shi ya sa ba na karba.”
Mohammed Isa mai kayan gwari shi ma ya ce, gara ya ki karbar tsoffin kudaden da ya bari su ja masa asara.
“Lokacin da aka fara cewa mu kai tsoffin kudin CBN, sai da na yi kwanaki a kofar CBN don in ajiye N100,000. Shi ya sa na yi wa kaina riga-kafi, da in yi asara gara kaya na sun yi kwantai.”
Yankin Kudu
Wannan yanayi haka yake a wasu sassa na Jihar Legas, inda bakuna suka fara bayar da tsoffin kudin, amma na dar-dar wajen yin cinikayya da su, duk kuwa da umarnin CBN na ci gaba da amfani da su zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
A Jihar Ribas kumma, manyan shaguna da gidajen mai da wasu wuraren kasuwanci na ci gaba da harkokinsu da tsoffin kudin.
Sai dai an korafi cewa duk da cewa bankuna na bayar da tsofifn kudaden, amma idan aka kai musu ba sa amsa.
Wata mazauniyar garin Fatakwal, Amaka Ike, wadda wakilinmu ya zanta da shi ya ce, ta ce da kyar ta iya yin sayayya da tsofifn kudaden.
Amaka ta ce, “wasu masu shaguna, gidajen mai da wasu ’yan kasuwa ba sa karbar tsoffin kudaden saboda a cewarsu, har yanzu ba su natsu ba, gwamnati za ta iya sauya shawara a kowane lokaci, kan batun.”