Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya bukaci kamfanonin wutar lantarki su dakatar da batun karin farashin wuta har sai sun wadata ‘yan Najeriya da mitoci.
Ahmed Lawan ya kuma nuna rashin gamsuwa da cajin kudin wutar da ake yi wa ‘yan kasa ba tare da la’akari ko lissafin iya abin da suka amfana da shi ba.
- Bai kamata talaka ya biya Naira 3000 kudin wuta ba
- An kara farashin man fetur zuwa N143.80
- Gwamnonin Najeriya da suka kamu da coronavirus
Ya yi jawabin ne bayan shi da takwaransa na Majalissar Wakilan Tarayyar Najeriya, Femi Gbajabiamila sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbanjo a fadar gwamnati a ranar Talata.
Idan ba a manta ba, Hukumar Kula da Wutar Lantariki ta Kasa (NERC) ta ce daga ranar 1 ga watan Yuni ne sabon kudin wutar lantarki zai fara aiki.
Amma Shugaban Majalisar ya ce lokacin bai dace a kara kudin wutar lantarki ba, duba da halin da ‘yan kasa suke ciki sakamakon annobar COVID-19.
Ya kuma ba da tabbacin jingine karin farashin wutar bayan sun cimma matsaya Hukumar Wutar lantarkin ta kasa.
“Mun zauna da kamfanonin raba wuta (Discos) da Hukumar kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) mun kuma fihimci cewar yanzu ba lokacin da ya kamata a kara kudin wuta ba ne.
Yanayin da ‘yan Najeriya ke ciki
“‘Yan Najeriya na cikin matsaloli iri-iri sakamakon annobar COVID-19 da ke bukatar mu yi bakin kokari mu saukaka musu rayuwa kuma gwamnati na iya kokarinta.
“Muna fata Discos za su ci gaba da wayar da kan jama’a, su kuma yi karin farashin da ba zai cutar da jama’a ba. Amma kafin hakan, ya kamata a tabbatar an raba wa masu amfani da wutar mitoci.
“Idan ba haka ba, za a rika hasashe wajen cajin mutane. Saboda haka ya kamata a rika amfani da kimiyya wajen gano wutar nawa mutum ya sha a kuma caji daidai ba tare da aringizo ba” inji Lawan.
Yarjejeniyar da aka yi da gwamnati
Ya ce kuma, idan har ana son wadatattar wutar lantarki a Najeriya, dole kamfanonin su aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da Gwamnatin Tarayya a lokacin sayar musu da kamfanin.
Yarjejeniyar ta hada da rashin tsawwala farashin wuta da kuma kara shi a lokacin da ya dace.
Da yake bayani, Gbajabiamila ya ce dukkanmu mun aminta a sa farashin ba cuta-ba-cutarwa, amma kuma a lokacin da ya dace.
Ya ce sun gana da Mataimakin Shugaban Kasa ne wanda shi ke jagorantar kwamitin wutar saboda ‘yan majalissa da bangaren zartarwa su hadu su yi aiki tare.
Ya ce da farko sun tattauna da shugaban kasa game da karin kudin duba da yanayin da ake ciki na annobar COVID-19, kuma ya ba su goyon bayan su hana kamfanonin kara farashin wutar.