✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sahabbai Goma ’yan Aljannah (2)

Haka Sayyadina Abubakar (RA) ya ci gaba da bayar da dukiyarsa wajen taimakon talakawan Musulmi da saukar baki da taimaka wa masu tafiya jihadi da…

Haka Sayyadina Abubakar (RA) ya ci gaba da bayar da dukiyarsa wajen taimakon talakawan Musulmi da saukar baki da taimaka wa masu tafiya jihadi da guzuri da abin hawa. Tarihi ba zai taba mantawa da abin da wannan Siddiki (RA) ya yi lokacin tafiya Yakin Tabuka ba. Da Manzo (SAW) ya nemi a kawo gudunmawa don tafiya wannan yaki, shi dukiyarsa ya kai baki daya. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce da shi, “Me ka bar wa iyalinka”? Sai ya ce: “Na bar musu Allah da ManzonSa (SAW)!”

Lokacin da Manzon Allah (SAW), ya yi wafati, hankalin Musulmi ya tashi kwarai, har wadansu suna cewa, Manzon Allah bai rasu ba. Sayyidina Abubakar (RA) duk da tsananin shakuwarsa da Manzon (SAW) shi Allah Ya bai wa karfin zuciya, ya fita ya yi wa jama’a huduba, wadda ta sanyaya jikin kowa, aka kuma hakikance cewa, Manzon Allah (SAW) ya koma ga UbangijinSa.

Sayyadina Abubakar (RA), shi Musulmi suko zaba, ya zama Khalifan Manzon Allah (SAW). Kuma duk da bai dade bisa wannan aiki ba, cikin shekaru biyu da ya yi yana Khalifa, ya yi muhimman ayyuka, wadanda ba za a taba mantawa da su ba a Musulunci.

Bayan wafatin Manzon Allah (SAW), kabilun Larabawa da dama sun yi ridda, (sun fita daga Musulunci). Wasu kuma suka hana Zakka. Aka samu wadansu shakiyyai da suka yi ta mara musu baya, Daga cikinsu, akwai Musailama Alkazzab da Dulaihat Ba’asabe da Aswadul Anissiy. Khalifa Abubakar (RA) bai yi wata-wata ba, ya shirya rundunonin yaki, a karkashin manyan sadaukai, irin su Khalid Bin Walid (RA), sai da ya ga bayansu. Aka kashe na kashewa (kamar Musailama) mafi yawansu kuma, suka tuba suka dawo Musulunci.

Bayan kwantar da tarzomar cikin gida, sai kuma ya shiga aikewa da mayaka don bude wasu kasashe da shigar da su karkashin daular Musulunci. Tuni dai ya zartar da tura rundunar da Usamatu dan Zaidu ke wa jagoranci, zuwa yaki kasar Sham (Siriya), wadda tun kafin Manzon Allah (SAW) ya yi wafati, ya shirya ta. Rashin lafiyarsa, ya dakatar da tafiyar. To, bayan gamawa da ’yan ridda da annabawan karya, Musulmi sun samu nasarar bude manyan garuruwa da shigar da su karkashin daular Musulunci. Farisa da Rum da Masar.

A zamanin Sayyidina Abubakar (RA) ne ya sa aka tara Alkur’ani, aka rubuce shi wuri guda, don gudun bacewar wani abu daga cikinsa, sakamakon samun mahaddata Alkur’ani masu yawa da suka yi shahaba a yakin ’yan ridda. Aka ajiya shi a wurin Uwar Muminai Hafsat ’yar Umar, (RA). Yayin da Sayyadina Abubakar (RA) ya fuskanci ajali ya matso masa, sai ya yi wasiyya a kan Sayyidina Umar dan Khaddabi (RA) ya zama Halifa a bayansa, bayan ya shawarci manyan sahabbai, da samun goyon bayansu kan haka.

Sayyidina Abubakar ya rasu ranar Litinin, 27 ga Jimada Akhir, shekara ta 13 Bayan Hijira, yana da shakara 63. An binne shi a dakin Nana A’isha (RA), kusa da Manzon Allah (SAW). Allah Ya kara musu yarda.

 

  1. Umar bin Khaddab (Allah Ya kara masa yarda):

“Da za a samu wani Annabi a bayana, da ya kasance Umar dan Khaddabi ne.”  – Manzon Allah (SAW).

Shi ne Umar dan Khaddabi dan Nufailu dan Addi dan Abdul Uzza dan Ribalu dan Abdullahi dan Kurdu dan Razahu dan Addi dan Ka’abu, Bakuraishe, Bamakhzume. Sun hada nasaba da Annabi (SAW). Ana yi masa alkunya da Baban Hafsa. Haka kuma Manzon Allah (SAW) ya kira shi da Faruku.

An haife shi a Makka, bayan shekarar giwa da shekara 13. Ya kasance, yana kiwon dabbobin mahaifinsa, lokacin da yake karami. Da ya girma sai ya shiga harkar kasuwanci, inda yakan je fatunci kasar Sham.

Kafin musuluntarsa, yana cikin makiya Musulunci da Musulmi, tare da azabtar da su. Sai Allah Ya karbi addu’ar Manzon Allah (SAW), ya shiyar da shi zuwa Musulunci. Musuluntarsa ke da wuya, sai ya jagoranci Musulmi, shi da Sayyadina Hamza (RA), Baffan Annabi (SAW) suka fito cikin garin Makka, suna kabbara kowa ya gansu. Tun daga locacin nan Musulmi suka daina buya, kan haka ne, Manzon Allah (SAW) ya kira shi da Faruku (mai rabe gaskiya da karya). Sayyadina Umar (RA) bai yi kaura zuwa kasar Habasha ba. Domin shi gagara-badau ne, kowa yana shayinsa a Makka. Lokacin kaura zuwa Madina kuwa, bai bar Makka a boye ba. Hasali ma, sai da ya sanar da manyan kafiran Makka cewa shi ya fita zuwa Madina, in har akwai mai jin zai iya hana shi, to ga fili ga mai doki! Ya halarci dukan yake- yaken daukaka Musulunci tare da Manzon Allah (SAW) cikin kowane yaki kuma yana ragargazar makiya Allah da ManzonSa (SAW). Duk taron kafiran da ya nufa sai ya tarwatsa su, yana cikin sahabban da suka tabbata tare da Annabi a filin Yakin Uhudu, yayin da  aka watsa rundunar Musulmi.

Sayyidina Umar (RA) shi ne tamkar Waziri na biyu ga Manzon Allah (SAW) bayan Sayyidina Abubakar. Sau da yawa Alkur’ani kan sauka yana tabbatar da abin da Umar (RA) ya ba da shawara a yi, kamar wajen haramta giya da ribatatun Yakin Badar da hijabi da wasu abubuwa da dama. Kan haka Manzon Allah (SAW) ya ce, “Yarda Allah tana cikin yardar Umar”. A lokacin Halifa Abubakar, shi ne babban Waziri gare shi. Shi ne ma ya bai wa Halifa Abubakar shawara a tara Alkur’ani a rubuce shi wuri guda. Kafin Halifa Abubakar (RA) ya rasu kuma ya yi wasiyyar ya zama halifa a bayansa. Musulmi kuma suka amince, ba tare da wata jayayya ba. An yi masa mubaya’a ran 22 ga watan Jimada Akhir shekara ta 13 Bayan Hijira. (23/8/634 Miladiyya).

Shi ne wanda aka fara kira da sunan Amirul Muninina. Shi ne ya fara amfani da tarihin Hijiriyya. Shi ne ya tara mutane, don yin Sallar Asham cikin watan Ramadan. Ya kuma sanya fitilu a masallatai. Shi ne farkon wanda ya ba da shawarar a tara Alkur’ani. Shi ne ya fara fita da daddare, don jin irin hallin da talakawa ke ciki. Shi ne farkon wanda ya raya birane ta hanyar shirya su da tsara su.

A zamanin halifancinsa, Musulmi suka karasa cinye biranen Sham da Iraki da Farisa, suka kuma bude birnin Masar da Palasdinu  tare da Baitul Mukaddis. Ta fuskar gudanar da daula kuwa, ya tsara abubuwa masu yawa da nagarta, don jin dadin al’umma. Shi ne ya fara amfani da “diwani” (Rajistar sunayen mayaka) da abin da za a rika bai wa kowane mayaki gwargwadon matsayinsa. Shi ne ya fara tura alkalai zuwa garuruwa. Da dai sauran tsare-tsare masu yawa.

Sayyidina Umar (R.A) adalin shugaba ne, wanda ba a samu kamarsa ba. Ga takawa da gudun duniya. Ya kasance yakan kara hannusa a wuta sai ya ce: “(Kunar) wannan?” Sai ya fashe da kuka. Har sai da ya zamo yana da wani zanen baki biyu na hawaye, a kumatunsa, saboda yawan kuka, don tsoron Allah.

Sayyadina Umar, ya rasu sakamakon suka da wuka mai dafi da wani Bamajuse Abu Lu’u-lu’a’tu, ya yi masa, yana Salla a masallaci, ran 23 ga Zul-Hajji, hijira na da shekara 23. An binne shi a dakin Nana A’sha (RA), kusa da Manzon Allah (SAW) da Sayyadina Abubakar (RA). Ya yi shekara 10 da wata shida yana halifa. Allah Ya kara masa yarda.

 

Imam Ahmad Adam Kutubi,

Nigeria Police Force,

Zone 7, Police Headkuarter,

Abuja. 08036095723