Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Ikko na Jihar Legas, ta yanke wa wani matashi mai shekara 20 hukuncin cin sarka na tsawon shekaru biyu.
A yayin zaman kotun da aka gudanar a ranar Litinin, an samu matashin da laifin safarar Tabar Wiwi da ta kai nauyin giram 400.
- Yadda ’yan Arewa ke kaura daga Ibadan bayan rikicin Sasa
- Wata sabuwa: Cutar Ebola na sake barazana ga Najeriya
- Ya kubuta daga hannun masu garkuwa da tabon harsashi a jikinsa
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito, aikata laifin ya saba da dokar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta kasa (NDLEA).
Mai shari’a Chuka Obiozor, ya bayyana cewa kotun ta yankewa matashin wannan hukunci ne bayan dalilan da aka gabatar mata wadda ta tabbatar da laifin matashin na safarar miyagun kwayoyi.
Jami’in dan sanda mai gabatar da kara, Mista Jeremiah Aernan, ya bayyana wa kotun cewa, an cafke wanda ake zargi da aikata laifin a ranar 23, ga watan Nuwamban 2020.
Mista Jerimiah ya ce an kama matashin ne yana hada-hadarsa da Tabar ta Wiwi a Unguwar Ile-Epo da ke yankin Ikorodu aa Jihar Legas.
Laifin safarar miyagun kwayoyi babban laifi ne da ya saba da sashi na 11(c) na kundin dokar Hukumar NDLEA, da kundin dokoki na kasa, sashi na 30 na shekarar 2004.