✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sadik Umar zai zama babban dan wasa – Siasia

Mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa ’yan kasa da shekara 23, Samson Siasia ya ce dan wasan kwallon kafa na AS…

Mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa ’yan kasa da shekara 23, Samson Siasia ya ce dan wasan kwallon kafa na AS Roma da ke kasar Italiya, Sadik Umar zai zama babban dan wasa da Najeriya za ta yi alfahari da shi nan gaba.
Sadik Umar, yana daya daga cikin masu neman gurbi domin buga wa Najeriya a gasar Olampik da za a buga a garin Rio Janeiro da ke kasar Brazil.
Mai horarwar ya kara da cewa “Bisa alamun da na gani a wurin gwaji, lallai Sadik zai zama babban dan wasa nan gaba musamman in ya ci gaba da da’a kuma ya ci gaba da kokari.”
Siasia ya kara da yi wa Sadik ta’aziyya kan rasuwar mahaifinsa bayan ya yi fama da doguwar jinya wanda hakan ya sa aka ba Sadik hutu domin ya je gida.
Siasia ya ce, “Sadik Umar yaron kwarai ne sosai, zai dawo da sauri domin mu ci gaba da shirye-shiryen da muke yi. Kuma Allah Ya jikan mahaifinsa.”
’Yan wasan dai sun yi wasan sada zumunta da kasar Meziko inda ta lashe su da ci daya mai ban haushi.