Tsohon Babban Alkalin Jihar Anambra, Farfesa Peter Umeadi, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kamo mutanen da suka sace daliban makarantar GSSS Kankara a jihar Katsina, ta kuma ga bayansu.
Umeadi, ya yi Allah-wadai da ta’addancin, yayin da yake ganawa da masu zaben fitar da gwani na Jihohi biyar da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, karkashin inuwar Kungiyar tuntuba ta Farfesa Peter Umeadi dake kudu maso gabas a garin Awka ta jihar Anambra.
- Kotun Koli ta rantsar sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya 72
- Majalisar Dinkin Duniya na bukatar a gaggauta sako daliban makarantar Kankara
- ’Yan daba sun tsarwatsa taron samar da tsaro a Arewa
“Zuciya ta kacokan na kan daliban GSSS Kankara, Jihar Katsina, wadanda a kwanan nan aka yi garkuwa da su.
“Ina kyautata zato da fatan yaran za su dawo gida cikin koshin lafiya kamar yadda iyayensu da gwamnati da dukkan ‘yan Najeriya suke fata.
“Ina takaicin abubuwan da suke faruwa marasa dadi a ko’ina a fadin kasar nan.
“Muna fatar samun mafita ta yadda za a kawo karshen faruwar hakan tare da gurfanar da masu aikatawa irin wannan laifuka a gaban shari’a don su girbi abun da suka shuka”, inji shi.
Jagorar kungiyar, Dokta Nkechi Ibeneme ta bayyana cewa, an kafa kungiyar ne da nufin tallata manufofin farfesa Umeadi.
Ta yi karin haske cewa, Ayyukan Kungiyar yafi tasiri a Jihohi biyar dake yankin Kudu maso gabashin Najeriya wanda nan ba da jimawa ba suke sa ran kaddamar da kungiyar da zata karade ilahirin yankin bakidaya.