Ranar Talata 11 ga Satumba, 2018 ce ta zama 1 ga Muharram wato ranar farko ta Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1440 Bayan Hijira.
Kalmar Muharram na nufin ‘Abu mai alfarma ko wanda ake girmamawa ko aka hana taba shi.’ Musulmi da dama na azumi a wannan wata. Ana lissafa kwanan watan Kalandar Musulunci ne bayan ganin wata, kuma ana ganin jinjirin watan ne bayan faduwar rana. Kwanakin Kalandar Musulunci a shekara sun kai 354 ko 355 a kowace shekara. kwanakin hutun shekara na iya sauya wa saboda ana samun ragin kwanaki daga 10 zuwa 12 da na Kalandar Girigori ko ta ’yan albashi. Don haka za a iya samun bambancin kwanaki a Kalandar Musulunci wadda bai daidai take da da Kalandar Girigori da ke da kwananki 365 zuwa 366 a shekara.
Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci ba kamar irin na karamar Sallah da Babbar Sallah ba ne, saboda Sabuwar Shekarar Musulunci ta kasance ranar tunawa da Hijirar Annabi Muhammad (S.A.W) daga Makkah zuwa Madina a shekarar 622 Miladiyya. Shekarar Musulunci wadda ake kira da ta Hijira ta samo asali daga Kalandar Musulunci.
Saboda watan Muharram ya kasance watan da wadansu Musulmi ke gudanar da azumi, duk da yake azumin bai zama wajibi ba, musamman a goma ga watan Muharram wanda ake kira da Ashura. Wannan rana ita ce ranar da Annabi Nuhu (AS) ya bar jirgin Ark kuma a cikinta aka ceto Annabi Musa (AS) daga Fir’una. Watan na daya daga cikin watanni hudu na Kalandar Musulunci da ba a yarda a yi fada a ciki ba.
Sabuwar shekarar tana nufin sabuwar dama a kan abin da mutum yake shirin yi. Ana nuna murnar sabuwar shekarar ba kamar sauran kwanakin da ake bukukuwa ba, ita ranar wannan sabuwar shekara ana yi addu’o’i da karanta Alkur’ani da gyara kura-kuran da aka yi a baya.
Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1440 Bayan Hijira za ta tuna wa sauran Musulmin Duniya yadda magabata suka gudanar da rayuwarsu don mu ma mu yi koyi da su. Amfani da Kalandar Musulunci zai zama wata madogara da za ta taimaka wa Musulmin Duniya neman ilimin addini da binciken tarihi.
Farkon Kalandar Musulunci alama ce ta nuna tarihin Musulunci kuma lokaci da al’umma za ta dauki darasi na canja rayuwar jama’a ta hanyar nuna ’yan uwantaka.
Sabuwar Shekarar 1440, Bayan Hijira alama ce ta Musulunci da take bambanta sauran al’umma da kuma tsara hanyoyin da ke da alaka da bauta kamar su: Zakkah da Azumi da Aikin Hajji wanda kalandar ta tanadar da lokutansu. Lokaci ne na gyara kura-kuran shekarun baya tare da yin godiya na shiga sabuwar shekara da yin aikin kusanci da Allah da bin umarninSa tare da kyautata wa sauran jama’a.
Akwai bukatar Musulmi su ci gaba da kiyaye dokokin Musulunci don su kasance masu gudanar da cikakkiyar rayuwa da sadaukar da kai a kan bauta kamar yadda addinin ya tanadar, ta yin amfani da Kalandar Musulunci a koyaushe ba kamar yadda kawai ake amfani kalandar wajen bukukuwan shekara ba. Mu na yi wa Musulmin duniya murnar shiga Sabuwar Shekara, muna kira su gyara kurakuran da aka yi a shekarar da ta gabata sannan a yi amfani da wannan bikin wajen yin adduo’in samun zaman lafiya da ci gaban Najeriya. Barka da Sabuwar Shekarar Musulunci.