A yayin da gwamna mai jiran gado, InjiniyaAbba Kabir yake ta shirye-shiryen karbar ragamar jihar mu ta Kano, ga ’yan shawarwarina a kan wasu bangarori na al’umma:
1. Dalibai:
Kowa ya san rawar da dalibai suka taka wajen zaben gwamna mai jiran gado wadanda yawancinsu matasa ne maza da mata.
Duk da cewa an jawo hankalinsu ne da maganar ilmi kyauta da kuma ba su damar karo karatu a kasashen waje, to amma mun san cewa ba kowa ne zai samu wannan ba.
Saboda haka a yi kokarin inganta makarantun gida tun daga firamare zuwa sama ta hanyar gyara makarantu.
Sannan a samar da kayan aiki da kuma bayar da tallafin karatu da daukar karin malamai, tare da kulawa da hakkokinsu da duk wani abu da zai taimaki tsarin koyo da koyarwa.
2. ’Yan fansho:
Tsawon shekaru kowa ya san matsalolin da tsarin fansho da giratuti yake ciki a yanzu wanda haka ya jefa rayuwar ’yan fansho da ta iyalansu a cikin halin damuwa da ya kai a wasu yankunan har wasu kungiyoyi aka samu na fusatattun ’yan fansho.
Yawancinsu sun mara wa sabuwar gwamnati baya ne saboda sa ran za ta share musu hawaye kuma Muna da masaniyar cewa gwamna mai jiran gado har ganawa ya yi da irinsu. Saboda haka ya zama wajibi a yi tsarin da zai taimake su.
Idan har gwamnati tana shirin yin “empowerment” to lallai biyan hakkin ’yan fansho shi ne farko domin kulawa da su daidai yake da kulawa da tarin iyalansu.
3. ’Yan kasuwa:
Kano cibiyar kasuwanci ce, don haka bunkasa kasuwanci a Kano yana da matukar muhimmanci wajen cigaban wannan yanki namu.
Sanin gudunmawar da ’yan kasuwa suke bayarwa yasa duk ’yan siyasa suke haba-haba da su lokacin yakin neman zabe ta hanyar rige-rigen yi musu jaje da alkawauran kulawa da harkarsu.
Wasu ’yan takarar ma har kasuwanni suke zuwa kamfe. Ko kauyuka ma yawanci sai an saita ranar kasuwar garin ake dira.
Saboda haka ya zama dole sabuwar gwamnati ta yi tsarin da zai taimaki kasuwanci da kuma kiyayar duk wani abin da zai kara tabarbara shi.
4. Kananan hukumomi:
Yana daya daga cikin koma-bayan da aka samu shi ne karya tsarin kananan hukumomi.
Kusan shekaru 12 ke nan da sarrafa kudaden kananan hukumomi kacokan ya koma hannun gwamnoni, wanda ya haifar da illoli da yawa ta bangaren ayyukan raya kasa da samar da ayyukan yi da ilmi da lafiya da rage kuncin rayuwa da inganta tsaro da sauransu.
Sanin muhimmancin kananan hukumomi ya sa jam’iyya mai shirin karbar mulki ta karade kananan hukumomi 44 da ke jihar nan a lokacin yakin neman zabe, kuma na tabbata sun ga halin da suke ciki kuma sun yi musu alkawura.
Muna bayar da shawarar cewa a dawo da martabarsu ko dai ta hanyar ba su ’yancinsu, ko kuma a yi musu tsarin da akalla za su ci moriyar kasonsu da ake turo musu daga Gwamnatin Tarayya.
A yi duba da cewa kowace karamar hukuma da abin da ta fi bukata domin kada a maimata kuskuren da aka yi a baya.
5. Sarakunan gargajiya:
Duk da juyin zamani, jagororinmu na sarauta suna da muhimmiyar rawa da suke takawa a matsayinsu na iyayen kasa.
Muhimmancinsu ne ya sa har gobe ake amfani da su wajen aiwatar da tsare-tsaren gwamnati da wayar da kai da harkar zamantakewa da tsaro da sauran su.
Wannan ya sa a lokacin kamfe ake kai musu ziyara.
Muna kira da sabuwar gwamnati da ta farfado da darajar wannan bangare, birni da kauye da kuma kokarin tsaftace shi don cigaban amfanar al’ummarmu.
6. Malaman addini:
Su ma malamai suna bayar da gudunmawa duba da aikin da suke yi na karantar da al’umma da kokarin bayar da tarbiyya.
Wannan ya sa babu wata gwamnati da ba ta amfani da malamai wajen gudanar da al’umma.
Muna yin tuni da a saurare su, kuma a kula da mutuncinsu da sakon da suke dauke da shi ga al’ummarmu.
7. Manyan gari:
Allah Ya albarkaci Jihar Kano da manyan mutane kama daga malamai da sarakai da attajirai da manyan ’yan boko da sauransu.
Suna amfanar al’umma ta bangarori da dama; Mun ga an kai musu ziyara lokacin kamfe kuma mun san sun bayar da gudunmawa a fili da boye.
Gudunmawarsu ga gwamnati mai jiran gado ba irin tamu ba ce. Da fatan za a ci gaba da neman su don cin moriyar girman da Allah Ya yi musu.
8. ’Yan jam’iyya:
Mutanen nan da gaske suke, ba dare, ba rana, ba ji, ba gani. Duk inda ka gan su aikin jam’iyya suke yi.
Ba cewa na yi su kadai ne suka bada gudunmawa ba, amma aikinsu na daban ne.
Muna kira da kada a wofantar da su.
A zabo masu jajircewa da amana a cikinsu, a saka su guraren da za su iya rikewa, sauran kuma a san yadda za a yi da su.
9. Mai Girma Kwankwaso:
Madugu Uban Tafiya! Fadar muhimmancinsa a wajen sabuwar gwamnati bata baki ne.
Yana da tunani da yawa a kan cigaban Kano kamar yadda aka gani a baya.
Lallai a saurare shi. A lallaba shi, kada a yi rigimar ba gaira ba dalili da shi.
Allah Ya taimaki Jihar Kano da kasa baki daya!