Hukumar kwallon kafar Turai (UEFA), ta nuna adawarta da sabuwar gasar European Super League, lamarin da ta ce duk dan wasan da ya shiga gasar ba zai buga gasar cin Kofin Duniya ba.
UEFA ta yi Allah wadai da shirin kafa sabuwar gasar da wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai da ake kira European Super League.
- Babu kudirin kara farashin man fetur a watan Mayu — NNPC
- An kaddamar da kwamitin bincike kan rikicin sarautar Tangale a Gombe
Shugaban UEFA, Aleksander Ceferin, ya yi gargadin cewa za a haramta wa duk dan wasan da ya buga gasar wakiltar kasarsa.
’Yan siyasar Turai ciki har da Firaministan Birtaniya Boris Johnson da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, sun yi Allah wadai da sabuwar gasar.
Kazalika, Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta ce, ba za ta amince da wannan sabuwar gasa ba, kuma duk wanda ya shiga cikinta, to za ta haramta masa buga gasar cin kofin duniya a cewarta.
Sai dai wadanda suka shirya sabuwar gasar sun ce za su dauki matakin shari’a domin tabbatar da kafa gasar.
Hukumomin kwallon kafa na Turai na ganin cewa, sabuwar gasar za ta yi illa ga Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, yayin da ma’assasan sabuwar gasar ke cewa, za ta kawo kudaden shiga fiye da ta cin Kofin Zakarun Turan.
Manyan kungiyoyin kwallon kafa 20 a Turai da suka hada da na firimiyar Ingila, Serie A, Bundesliga, Ligue 1, Primeira Liga, Firimiyar Rasha da kuma La Liga ne ke shirin fara buga gasar a tsakiyar mako, duk da cewa za su ci gaba da buga wasanninsu na gida da suka saba.
A yanzu dai tuni wasu attajirai da suka hada da manyan kamfanoni da bankuna suka bayyana aniyarsu ta zuba jari a sabuwar gasar saboda kwadayin ribar da za su samu.