An kara sassauta dokar hana fitar da aka sanya saboda coronavirus a jihar Kano zuwa kwana uku a duk mako.
Za a bude wuraren ibada da kasuwanni da sauran harkoki a ranakun Laraba da Juma’a da kuma lahadi daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Gwamnatin jihar ta wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai Muhammad Garba ya fitar ta gindaya sharuddan kasuwanni da wuraren ibada za su cika.
Umurnin ya wajabta rufe fuska, da samar da abun wanke hannu da kuma auna yanayin zafin jiki a wuraren ibada da kasuwanni.
- Azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya
- Bam ya kashe wani yaro dan gudun hijira a Borno
- Abin da kungiyoyin addinai suka ce kan bude wuraren ibada
Hakan ya biyo bayan ganawar da gwamnatin jihar ta yi ne da shugabannin addinai da ‘yan kasuwa da kwararru a fannin lafiya.
Sai dai kuma makarantu za su ci gaba da zama a rufe a fadin jihar, kazalika sufuri tsakanin jihar Kano da wata.
Gwamantin jihar ta shawarci ‘yan makaranta da su rika bin darussan da ake sakawa a gidajen radiyo ta talabijin loto-loto a jihar.