✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon rikici ya ci mutum 11 a Jihar Filato

Akalla mutum 11 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a wani sabon hari da aka kai a kauyukan bat da Zakupang da…

Akalla mutum 11 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a wani sabon hari da aka kai a kauyukan bat da Zakupang da Foron da ke karamar Hukumar Barikin Ladi a karshen makon jiya a ci gaba da rikicin da ake samu a yankin.

Kakakin rundunar tsaro ta musamman a Jihar Filato (STF) Kyaftin Ikedichi Iweha ya tabbatar da kai hare-hare da kuma kashe mutum 11.
Kyaftin Iweha ya ce hare-haren ana zargin Fulani ne suka kai su, bayan da aka sace musu shanu sama da 500 a yankin a kwanakin baya. Ya ce a lokacin da aka sace shanun rundunar tsaro ta yi iyakar kokarinta wajen gano shanun da aka sace, inda ta gano 282 ta kuma mayar wa makiyayan.
Ya ce zuwa yanzu hankula sun kwanta a yankunan da aka kai hare-haren kuma rundunar tana iyakar kokarinta, don gano wadanda suka kai hare-haren.
To, amma a nasa bangaren Shugaban karamar Hukumar Barikin Ladi, Emmanuel Lomang ya ce maharan sun kashe mutum 17 ne a hare-haren da suka kai kauyukan bat da Zakupang da Foron da ke yankin.
A zantawarsa da ’yan jarida kan lamarin, shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa ta Miyyeti Allah reshen Jihar Filato Alhaji Haruna Boro Usaini ya musanta zargin da aka yi cewa Fulani ne suka kai hare-haren, ya ce domin Fulani ba su da wata damuwa da mutanen yankin. Ya ce a saninsa an samu shanun da aka sace a yankin kuma Fulani sun yi murna. Ya ce kabilun Birom ne suka taimkka aka samu shanun, saboda haka babu yadda Fulanin za su tashi su kai musu hari.