✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon rikici ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a masallacin birnin Kudus

Kusan duk shekara a kan samu irin wannan rikicin tsakanin bangarorin biyu da azumi

Wani sabon rikici ya sake barkewa a ranar Juma’a tsakanin ’yan sandan Isra’ila da masu zanga-zangar Falasdinawa a harabar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus.

’Yan sandan na Isra’ila dai sun kutsa harabar masallacin, inda matasan Falasdinawa suka yi ta jifansu da duwatsu, lamarin da ya kai ga jikkata mutane da dama.

A duk shekara, musaman lokacin azumin Ramadan, ana fuskantar irin wannan tashin hankali tsakanin Isra’ila da Falasdinawa da ke ci gaba da neman ’yanci daga mamayar yankunansu da Isra’ila ke ci gaba da yi.

Zanga-zangar ta yadu zuwa garuruwa da dama a gabar yammacin kogin Jordan da kuma kan iyakar Isra’ilan da Gaza.

Sojojin Isra’ila sun ce sun tarwatsa daruruwan Falasdinawa, yayin da wasunsu suka dinga jifansu da duwatsu da kuma kona tayoyi.

An dai samu tashe-tashen hankula da daddare tun bayan fara azumin watan Ramadan a daidai lokacin da Falasdinawa ke nuna bacin ransu kan yadda ’yan sanda suka toshe hanyar shiga filin shakatawa na katangar tsohon birnin da kuma hana taruka.

Rikicin baya-bayan nan tsakanin ’yan sandan Isra’ila da Falesdinawa a masallacin na Al-Aqsa ya yi sanadin jikkata sama da mutum 200.

Falasdinawa dai na ci gaba da Allah-wadai da wasu Shugabannin kasashen Larabawa da ke goyon bayan Isra’ila.