Sabon Kwamandan Rundunar Samar da Zaman Lafiya ta OPSH a Jihar Filato da Bauchi da Kaduna, Manjo Janar Anthony M. Atolagbe ya kama aiki.
Manjo Janar Atolagbe wanda aka canja wa wurin aiki daga Hedikwatar Tsaro da ke Abuja a matsayin Daraktan Wanzar da Zaman Lafiya ya maye gurbin Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas ne, wanda yanzu aka mayar da shi Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya a matsayin Babban Jami’in Sufurin Kayan Yaki.
A lokacin da ake bikin mika ragamar aiki a Hedikwatar OPSH a Jos ranar Asabar da ta gabata, tsohon kwamandan ya ce ya cimma gagarumar nasara, domin zai bar Jihar Filato fiye da yadda ya same ta a bangaren zaman lafiya.
Ya ce a lokacin da aka kawo shi jihar abubuwa a tabarbare suke, amma sakamakon tsayawa kai-da-fata da shi da rundunar suka yi, yanzu an samu ingantaccen zaman lafiya a jihar, kuma babu wanda zai yi musun haka. “Kasuwanci na ci gaba da bunkasa, an samu raguwar fada a tsakanin manoma da makiyaya, rikicin kabilanci ya ragu sosai, fiye da wata bakwai ba a samu batun satar shanu ba, don haka zan iya cewa a batun zaman lafiya, zan bar Jihar Filato fiye da yadda na same ta,” inji shi.
A lokacin da Manjo Janar Anthony Atolagbe ke jawabi, ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen ganin cewa dakarunsa sun yi aiki tukuru wajen samar da zaman lafiya mai dorewa, zai kuma tabbatar da sun bi ka’idar aiki ba tare da nuna fiffiko ga wata kungiya ko bangare ko wani addini ba.“Na yi alkawarin zan yi bakin kokarina wajen ganin cewa duk dakarun da muka tura su wurin aiki ba su yi wani abu da zai bata musu suna ba, ko a yi zarginsu da nuna fiffiko ga wani addini ko bangare ko wata kungiya ba. Zan tabbatar da sun bi ka’idar aikinsu sau-da-kafa wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a wurare da yankunan da aka dora mana alhakin karewa,” inji shi.
Ya ce burinsa a ce a lokacin da ya kammala aikinsa sojoji su koma bariki saboda zaman lafiya ya zauna da kafafunsa. A karshe ya roki jama’a su ba shi hadin kai don ganin an ci gaba da zamun zaman lafiya mai dorewa a jihar.