✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon jerin sunayen barayi zai girgiza ’yan Najeriya-Lai Mohammed

  Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed jiya ya ce kwanannan Gwamnatin Tarayya za ta sake fitar da wani sabon jerin sunayen barayin…

 
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed jiya ya ce kwanannan Gwamnatin Tarayya za ta sake fitar da wani sabon jerin sunayen barayin kudin gwamnati kuma za a fallasa sunayen mutanen da ba a zata ba.
 
Ministan ya ce babu wata barazana da za ta dakatar da fitar da sunayen.
 
Ya bayyana haka ne a garin Ilorin yayin da yake ganawa da manema labarai a kan hanyarsa ta zuwa Abuja bayan ya je yin jaje ga gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed, da mutanen garin Offa da rundunar ’yan sanda da kuma  wadanda suka jikkata kan fashi da makamin da aka yi a garin a ranar Alhamis inda ’yan sanda bakwai da wadansu mutane suka rasa rayukansu sannan da dama suka sami raunuka.
 
Ya ce “Ba za mu dakatar da wadanda suke son zuwa kotu ba amma muna sanar da su cewa su sake yi wa kansu hisabi saboda yayin da gwamnati ta fitar da jerin sunayen tana da hujjojin da ta dogara da su”.