✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon harin Rasha ya kashe mutum 18 a Ukraine

Akalla mutum 18 sun mutu wasu da dama sun jikkata bayan Rasha ta yi ruwan rokoki a kan wasu biranen kasar Ukarine.

Akalla mutum 18 sun mutu wasu da dama sun jikkata bayan Rasha ta yi ruwan rokoki a kan wasu biranen kasar Ukarine.

Mata da kananan yara na daga cikin mutanen da harin rokokin Rashan ya hallaka a safiyar Juma’a a Kyiv da wasu biranen kasar.

Hukumomin Ukraine sun ce harin da Rasha ta kai wa birnin da Kyiv da sauransu, ya yi ajalin wasu mutum 16 a wani bene da ke tsakiyar birnin Uman, sai wata mata da ’yarta mai shekara uku da aka kashe a birnin Dnipro.

Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce benen da aka rusa a Uman daya ne daga cikin gidaje 10 da harin ya lalata ta birnin.

Zelensky ya kara rokon kasashen duniya da su gaggauta daukar tsauraran matakan da ya dace a kan Rasha.

Ma’aikatar Tsaron Rasha ta tabbatar hare-haren, inda ta ce hadafinsu shi ne sansanonin dakarun Ukraine na ko-ta-kwana kai tsaye.

Shugaban rundunar sojin birnin Kyiv ya ce harin farko ke nan da Rasha ta kai wa birnin a kwana 51 da suka gabata.

Ya ce sun kakkabo 20 daga cikin jirage marasa matka 23 da Rasha ta kai harin da su ba, amma bai ba da alkaluman mutanen da aka kashe ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe magajin garin Donetsk wanda Rasha ta nada tare da wasu mutum bakwai a wani hari atilare da sojojin Ukraine suka kai wa wata mota.