Gwamnatin Jihar Filato ta sake dawo da dokar hana fita ta sa’a 24 bayan sabon harin da aka kashe mutum 30 a kauyen Yelwan Zangam na Karamar Hukumar Jos ta Arewa.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce dokar hana fitar za ta fara aiki ne daga karfe 4 na ranar Laraba 25 ga Agusta, 2021, har sai abin da hali ya yi.
- An kama mutanen da suka kai sabon hari a Jos
- ’Yan bindiga sun kai hari NDA, sun kashe soja, sun sace hafsoshi
Gwamnan Simon Lalong ya umarci jami’an tsaro da su tsare duk wanda ya saba dokar hana fitar, sannan ya bukaci jama’ar yankin su kasance masu da’a ga umarnin.
Lalong ya jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su, ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su guji daukar doka a hannunsu, saboda a cewarsa, gwamnatin na yin abin da ya dace domin kare rayuwa da dukiyoyi.
Sanarwar da Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar, Makut Simon Macham, ya fitar ta ce yin hakan ya zama tilas, domin tabbatar da doka da oda, saboda barazar da rayuka da dukiyoyi suke fuskanta a Karamar Hukumar.
A cewarsa, hakan zai kuma ba wa jami’an tsaro damar gudanar da aikinsu na ganowa da kuma kamo wadanda suka kai harin, yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa har yanzu dokar hana fita da daga karfe shida na yamma zuwa 6 na asuba da aka sanya a Karamar Hukumar Jos ta Kudu na nan tana aiki.
Ya ce babu wanda aka daga wa kafa kafa, sai ma’aikata na musamman da jami’an tsaro, su ma din su tabbata suna dauke da sahihan alamun shaida a kodayaushe.